Mataimakin Gwamnan Katsina Ya Ankarar Da Masu Aikin Safiyo Su Tsare Ka’idojin Aiki

0
514
Imrana Mustapha Abdullahi
MATAIMAKIN Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Manir Yakubu, ya fadakar da masu aikin Safiyo da su ci gaba da tsare dokar aiki da duk wata ka’ida.
Ya bayyana masu cewa tsare dokar aikin muhimman al’amari ne kwarai a lokacin aiwatar da aikin a koda yaushe a cikin Jihar da kuma kasa baki daya.
Mataimakin Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron majalisar kolin kungiyar masu aikin Safiyo na reshen Jihar katsina, inda ta tabbatar masu cewa aikin su shi ne taimakawa a bangarensu wajen gina kasa don haka akwai bukatar a tsare ka’idojin aikin sosai a duk lokacin da ake aiwatar da aiki.
” Sai ya yi kira ga mambobin kungiyar masu safiyon a Jihar katsina da kasa baki daya da su bi ka’idoji da dukkan tanaje tanajen aikin domin hakan zai taimaka kwarai wajen fayyace dukkan gaskiyar al’amura musamman ta fuskar gina kasa da ciyar da ita gaba”.
Ya kuma shawarci yayannkungiyar da su kara kaimi domin ganin an samu ci gaba a reshen Jihar Katsina sai ya yi kira da bangarori masu zaman kansu da daukacin jama’a da su rika amfani da shawarwarin kwararru musamman masu aikin safiyon filaye domin samun biyan bukatar da suke nema wajen aikin da za su yi ta yadda za su more kudinsu.Yin haka zai taimaka wajen hana rushewar Gine ginen da ake samu lokaci ko bayan an yi gini.
Tun da farko shugaban kungiyar na kasa Abba Mohammad Tor, gode wa yayan kungiyar ya yi reshen Jihar Katsina game da irin yadda suka hada kansu aka samu mika jagoranci daga wasu shugabannin zuwa wasu a Jihar
Sai ya ankarar da sababbin shugabannin da su hanzarta aiwatar da Sabunta shaidar zama dan kungiya na shekara shekara da kuma bayar da horo ga yayan kungiyar tare da tsare dukkan ka’idojin da aikin Safiyo ya tanada.
Ya kara da bayyana muhimmancin tsare mutunci da martabar aikin na Safiyo da kuma yi wa sababbin mambobi rajista a reshen na Katsina.
An dai bayar da takardun shaida na satifiket da kuma lambobin karramawa da shugabanni tare da yi wa kowa fatan alkairi a rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here