Tube Sarki Sanusi II Umarnin Buhari Ne’ – Kwankwaso

0
483
Rabo Haladu Daga Kaduna
TSOHON Gwamnan Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya dora alhakin tube Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu kan shugaba Muhammadu Buhari.
Jigon adawar, ya ce “shugabannin gwamnati na Kano su da kansu ne ke cewa umarni aka ba su (su tube sarki Sanusi). Shi ya ba su umarni”.
Ya yi zargin cewa sabanin maganganun da makusantan Buhari ke cewa, shugaban ba ya tsoma baki cikin irin wadannan rigingimu, “sai dai musamman mu nan a Kano yadda muke gani (Buhari) yana hargitsa inda yake sa hannu”.
“Shugaba Buhari yana tsoma hannu cikin al’amuran jihar Kano”, in ji Kwankwaso. “Inda ya kamata ya sa hannun sai mu ga ba nan ya sa hannu ba, inda kuma bai kamata ya sa hannu ba, sai mu ga a nan yasa hannu.
Tun bayan da aka cire Sarkin a ranar Litinin, gwamnatin Buhari a hukumance ba ta ce komai ba akan batun. Sai dai a makonnin baya Shugaba Buhari ya ce ba zai haka baki a harkokin cikin gida na jihar Kano ba.
Sai dai  ba a samu bayanai daga wasu kafofi masu zaman kansu ba da ke tabbatar da ikirarin Sanata Kwankwaso.
Kwankwaso, wanda a zamanin mulkinsa ne cikin shekara ta 2014 aka nada Sarki Muhammadu Sanusi II, yana wannan kalami ne lokacin zantawarsa da manema labarai  a kan batun cire tsohon sarki.
A ranar Litinin ne, gwamnatin jihar Kano ta sanar da tube rawanin basaraken, tare da korarsa daga Kano zuwa garin Awe cikin jihar Nasarawa, inda ake ci gaba da killace shi.
Tsohon gwamnan Kanon ya ce tube sarkin Kano, wani abin bakin ciki ne ga jihar Kano da Najeriya da ma duniya gaba daya, “dama shi mai martaba sarki, mutum ne na duniya gaba daya”.
A cewarsa daga abin da suka ji da abin da suka gani, ko shakka babu gwamnatin da ta san ya kamata ba za ta tube Muhammadu Sanusi ba.
Muhammadu Sanusi II, basarake ne mai yawan janyo ka-ce-na-ce kuma tun a lokacin mulkin Kwankwaso ya fara kai ruwa rana da gwamnatin jihar, har ta ba shi takardar gargadi karo biyu.
Sai dai Kwankwason ya musanta hakan, inda ya ce “ni ban taba ba Mai martaba sarki wata takardar gargadi ko ma wani abu irin wannan ba”.
Haka kuma an tambaye shi game da zargin da ake yi wa magoya bayansa ‘yan Kwankwasiyya wajen rura wutar rikici tsakanin Sarki Sanusi da Gwamna Ganduje, nan ma tsohon gwamnan ya ce su ba sa goyon bayan kowa sai bangaren gaskiya.
Ya ce a iyakar saninsa kamar yadda “su kansu mutanen gwamnati ke fada”, Sarki Sanusi ya gamu da fushin Ganduje ne saboda sun ce basaraken ya ce duk wanda ya ci zabe a Kano, a ba shi nasararsa.
Kwankwaso ya kuma koka kan abin da ya ce wulakancin da aka yi wa jama’ar jihar Kano ta hanyar wulakanta tsohon sarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here