An Yi Rashin Dalibi 1 Yayin Da Gobara Ta Tashi A Makarantar Albany

0
425

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

SHUGABANNIN makarantar Albany International School, Zariya sun tabbatar da mutuwar dalibi daya dan ajin sakandare 3 mai suna Abdurahman Doko, a gobarar da ta tashi a dakin kwanan daliban makarantar ranar Laraba.

Gobarar wacce ta fara misalin karfe 2 na rana ta kona dakin kwanan dalibai maza da ke unguwar Gaskiya Layout.

Daraktan makarantar, Dakta AbdulRaheem AbdulGaniyu, ya bayyana cewa har yanzu ba a san abinda ya janyo gobarar ba.

Ya ce “A lokacin da gobarar ta fara, babu wuta a makarantar, kuma ba a yarda da girki a dakunan kwanan dalibai ba.“

“Dakin girkin abinci na da nisa da wajen kwanan. Saboda haka, ba mu san yadda abin ya faru ba.“

Diraktan ya yaba wa jami’an kwana-kwana kan amsa kiran da suka yi na gaggawa da kuma takaita gobarar.

Abdulganiyyu ya kara da cewa daliban makarantar na hutu illa daliban karshe da ke shirin jarabawar WAEC da UTME, da kuma masu shirin Junior WAEC kenan.

A cewarsa, a lokacin da gobarar ta far, dukkan daliban na azuzuwansu lokacin da gobarar ta kama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here