Sarki Sanusi II Ya Karbi Mukaman Da Aka Ba Shi A Kaduna – El-Rufai

0
546

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNA Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce tsohon sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II da aka sauke ya amince da nadin mukamen da ya yi masa a gwamnatin jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa Sanusi ya sanar da amincewa da karbar mukamin ne cikin wata sanarwa mai dauke da saka hannun hadimin Gwamna El-Rufai, Muyiwa Adekeye a ranar Laraba 11 ga watan Maris.

Gwamnan ya mika godiyarsa ga tsohon sarkin saboda ci gaba da bayar da goyon bayansa domin ganin jihar ta Kaduna ta cimma burinta.

A baya mun bayyana muku cewa gwamnatin jihar Kaduna a ranar Laraba ta karrama tsohon sarkin da wani mukammi.

An nada tsohon sarkin a matsayin shugaban gudanarwa na jami’ar jihar Kaduna (KASU).

Sanusi zai maye gurbin Tagwai Sambo, Sarkin Moro’a, wanda shi ne shugaban gudanarwa na jami’ar tun da aka kafa ta a shekarar 2005.

An kuma nada Sanusi a matsayin mamba na hukumar inganta saka hannun jari na jihar ta Kaduna wato (KADIPA).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here