Babbar Matsalarmu A Gwarzo Ita Ce Ruwan Sha – Ciyaman Kutama

  0
  1141

  MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba

  Kwanan baya wakilin mu na kudanci MUSA MUHAMMAD KUTAMA Ya ziyarci jihar Kano ya yada zango hedkwatar karamar hukumar Gwarzo inda ya zanta da shugaban karamar hukumar Gwarzo Injiniya Bashir Abdullahi Kutama .Kan matsalolin da suka fi ciwa karamar hukumar tuwo a kwarya injiniya Bashir Abdullahi Kutama,  yace matsalar ruwan sha ita  ce tafi damun karamar hukumar sa .

  Ga yadda tattaunawar su ta kasance

  GTK :Mai girma shugaban Karamar Hukumar gwarzo yi mana tsokaci kan irin matsalolin da karamar hukumar ke fama dasu,ka ke son kaga ka magance su?

  Injiya Bashir Kutama:Auzubillahi minashshaidanir Rajim BismillahirrRahmanir Rahim.Alal hakika babbar matsalar  da muke fama da ita a karamar hukumar Gwarzo matsala ce wacce bata   wuce ta Ruwan Sha, ba.

  GTK:Da kace matsala ce ta Ruwan Sha kana son gina madatsun ruwa ne ko kamar yaya kake son shawo kan matsalar da magance ta?

  Injiniya Bashir Kutama: A Karamar hukumar Gwarzo muna da madatsun ruwa guda  27.Tunda na zo a mulki guda 27 din nan kwaya biyu ne wadanda suke iya ajiye ruwa sauran guda 25 din kuma duk sun yage shekara-dashekaru basa aje Ruwa a dalilin haka munyi ikar bakin kokari muga mun gyara a kalla kamar kwara uku a yanzu sun samu Ruwa ,kuma  da taimakon Allah mutanen  gari sun gyara guda biyu a Kasar Lakwaya,idan kikayi la’akari da yanayin tattalin arzikin kasa zaki ga koda yaushe an habaka Noman rani a karkara domin gujewa matasa tafiya cin-rani kwarara cikin birane,kasancewar karamar hukumar Gwarzo tana cikin matsala wanda da zasu samu tagomashi gyaran wadan nan madatsun ruwan  namu alal hakika zai taimaka wajen warware matsalolin ruwan sha na karamar hukumar Gwarzo sannan ya samar da ayyukan Noman rani .

  GTK:Kai ne zababben shugaban wannan karamar hukumar a wannan lokacin naka ne aka samu wannan  matsala ko kuwa ka gaje ta ne?

  Injiniya Bashir Kutama:Duk kanin wadannan matsalaloli mun gaje su daga shugabancin baya ,kuma wani abin takaici gwamnatocin baya basu tabo suba  ina tabbatar maka tun lokacin tsohon mataimakin Gwamna Alhaji Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo yana matsayin shugaban karamar hukuma daya  giggina wadan nan madatsun ruwan basu kara samun gyara ko wata kulawa ba har sai wannan lokacin wannan  itace ta jefa wannan karamar hukumar cikin matsalar ruwan sha da muka tsinci kan mu a ciki .

  GTK :kace akwai madatsun ruwa har guda 27 ragowar 25 din zaka inganta su ne musamman aniyar ka ta sanya ‘yan karamar hukuma yin noman rani domin kada su rika zuwa cin-rani birane?

  Injinya Bashir Kutama :Alal hakika wannan shine kudiri na shine a raina kullum inda mun samu sahalewar yadda zamu gyara su .Matsalar mu anan kullum shine sanin kowa ne matsalolin da kananan hukumimi ke fuskanta a Najeriya yanayin yadda suka tsinci kan su wanda da muna da cikakken iko d isassun kudi to da yanzu sun zama tarihi domin yanzu kudin da mukan samu Magana ce ma ta yaya zakayi ka biya albashi.

  GTK:Bayan matsalar ruwan sha ana korafi hanyoyin mota sun lalace musamman na manyan garurukan karamar hukuma wane yunkuri maigirma shugaban karamar hukuma keyi don magance wannan matsala itama?

  Injiniya Bashir Kutama:Alal hakika daga wannan matsalar ta ruwan sha insha Allah sai kuma ta hanyoyin mot azan tunkara domin magance su musamman hanyoyin mota da manoma zasu rika dauko amfanin gona suna kawowa kasuwa sayarwa shekara-da shekaru akwai Gadojin da suka yayyanke akwai garurukan da ma sun yanke babu hanyar ma kwata-kwata wanda za’a iya cewa za’ayi amfani dasu.Zamana shekara biyu a mulkin aramar hukumar Gwarzo a kalla na gyara hanyoyin mota dai-daidai sun haura guda 10.Kuma na gyara Gadoji-Gadoji sun kai guda 15.A karamar hukumar Gwarzo, wanda mun shiga da fushin wannan abin cikin ikon Allah mun samu sahalewar  zababben  gwamnan jihar Kano Kadimul-Islama Dokta Abdullahi Umar Ganduje,muka gyara wadan nan wurare don mutane su samu yadda zasu kawo amfanin gonar su zuwa manyan garurukan dake wannan karamar hukuma

  GTK:Maigirma shugaban karamar hukumar Gwarzo baya ga wadancan matsaloli da ka zayyana ko a hukumance ka sanar wa gwamnan jiha halin da karamar hukumar take ciki?

  Injiniya Bashir Kutama:Alal hakika duk kanin matakai duk kanin hukumomi na gwamnati muna ta bi wanda a wannan dalilin ya sanya muke samun nasarar da muka samu  na iya gyara dimbin wadan nan gyare-gyaran da muka yi a yanzu .Don haka mun sanar dukannin wata hukuma wadda yake ta danganci wannan harkar Bangare-bangare bangaren ruwan sha ne ta bangaren hanyoyi ne muna sada wannan  bukatu na alumma da ita domin ganin an rabauta an fita daga cikin wadan na matsaloli.

  GTK:Kwanan baya maigirma gwamnan jihar  kano yayi nasara a shari’ar da yayi tsakanin sa da jamiyyar Adawa  ya kaji da wannan nasara da ya  samu?

  Injiniya Bashir kutama:Alal hakia babban dadin da naji shine kasancewar jiha ta da karamar hukuma ta ,ta Gwarzo zasuci gaba da shan romon Demokradiyya musamman  hikimomi da dabaru  na bayar da karfi kan harkokin tsaro da mai girma zababben gwamnan  jihar kano keyi wanda a tarihi sama da shekara 50 jihar kano bata taba tsintar kanta yadda ta more harkar zaman lafiya baga bako da dan gari irin yadda ake zaune lafiya kamar jihar kano ba musamman irin ibtilalo’in da ke faruwa a makwabtan jihohi amma cikin Ikon Allah jihar Kano ta  rabauta daga cikin wadan nan jihohi .Kuma kada ka mance karamar hukuma ta ta  kasance ina makwabtaka da jihar katsina ina kan iyaka babbar hanyar data tashi daga kano tabiyo karamar hukuma ta itace ta ta zarce har zuwa jihar Zamfara, ta karamar hukuma ta,ta keta muna zaune lafiya duk kanin matsalolin tsaro jami’an tsaro na bakin kokarin su ana zaune lafiya da wadancan rigingimun da balae-balaen basuyi tasiri a wannan karamar hukuma ba cikin ikon Allah an dan samu ‘yan matsaloli amma jami’an tsaro sun shawo kan matsalolin an magance su haka ne ya kawo karshen wannan abu wanda babu dare-babu rana to idan nayi la’akari da wannan na duba sai inga cewa al’ummar jihar Kano  sune suka samu nasara ba wai maigirma zababben gwamnan jihar Kano ba kadai .

  GTK :Sakon ka ga al’ummar karamar hukumar ka?

  Injiniya Bashir Kutama: Kira zanyi ga al’ummar karamar hukumar Gwarzo shine su kula da duk kanin vata gari ,duk kanin baki da duk kanin wadanda zasu shigo domin ganin cewa karamar hukumar mu ta zauna lafiya an samu ingantaccen tsaro .Bayan wannan zanyi kira ga ‘yan uwana matasa musamman wadanda suka baro jihohin nan na kudu musamman jihar Legas harkar nan ta haya Acaba ko Okada ganin cewa dawo mana da sukayi su zauna lafiya,su tabbata basu dawo mana da wani bakon al’amari ba don cutar da sauran matasan mu ba don haka ina yin kira su nemi sanao’I wadanda zasu dace da zaman su a wannan yankuna namu domin gani cewa sunci gaba sun bunkasa suma suba karamar hukuba ma tasu gudunmuwa.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here