A SAKAMAKON wa’adin kwana uku da hukumar tsare-tsaren gine-gine na birane da kauyuka wato KASUPDA na jihar Kaduna ta aika wa ‘yan kasuwar Barci, bayan wa’adin kwana ukun ‘yan kasuwar sun dukufa kwashe kayan sana’ar su da cire kayayyakin gine-ginensu da kansu bayan ganin an turo da motar gireda da ta fara rushe gine-ginen da ke kasuwar da karfe biyun dare.
Ita dai wannan kasuwa ta kasance daya daga cikin tsofaffin kasuwannin da ke cikin garin Kaduna wanda mafi akasarin ‘yan kasuwar suna sana’ar sayar da kayan gwanjo ne wanda yake shi ne karfin kasuwar da sana’ar da aka fi yin na’am da ita a wannan kasuwar.
‘Yan kasuwar wadanda bayan wa’adin na kwana uku da hukumar ta aika musu suka yi wa ganin kamar almara ce sakon takardan, sun tsinci kansu ne tsamo-tsamo a cikin aikin tattara kayansu da cire duk wasu mahimman kadarorinsu na kayan gine-gine ba arziki gudun kada asara ta yi musu yawa.
Wata majiya daga bakin wasu ‘yan kasuwar ta bayyana wa wakilinmu da ya kai ziyarar gani da ido cewa suna kwance a gidajensu a wannan daren ranar Lititin inda wasu makusanta kasuwar da masu gadin kasuwar suka rika kiransu a wayoyi don bayyana musu cewa an tsinkayi zuwan ita wannan motar rushe ginin wacce take kokarin rushe wasu shagunan.
Ta kara da cewa jin hakan ne ya sanya mafi akasarinsu da ba su riga sun kwashe kayayyakinsu ba suka garzaya kasuwar don kwashe kayan kamin washe gari ranar Talata su dukufa cire wasu abubuwan da suke ganin suna da mahimmanci a jikin gine-ginen su kamar irin kofofinsj masu tsada.
Ta ce ” da ganin yar motar cutar ta iso, shi ne sai aka sanar da daya daga cikin shugabannin kasuwar ta mu wato Dabai wanda a lokacin ya yi kokarin zuwa don yin magana da shi shugaban hukumar wanda tare da shi aka zo yin aikin da wasu jami’ai, kuma Allah cikin ikonSa Ya sa ya amince da rokon da aka yi masa wanda hakan ne ya sa ba a ci gaba da rushe shagunan ba har muka zo muka fara kwashe kayanmu.”
Majiyar ta kara da cewa babu shakka sun tabbatar da aukuwar yuwar hakan ta rushe kasuwar tun daga lokacin da suka ga gwamnatin Jihar ta fara bibiyarsu a kan sanin irin yadda tsarin kasuwar take, kana da biyan kudin haraji wanda mafi akasarin yan kasuwar ba sa biya, sannan aka bukaci kowannen su da ya tanadi takardar shaida ta mallakar shagunan nasu bayan sun ba da kwafi.
Acewarta, basa adawa da yin aikin ginin sabuwar kasuwar toh amma rashin sama musu wata matsuguni inda za su kasa kayansu har Allah Ya sa a kammala aikin ginin kasuwar ne ya sanya su shiga cikin matsanancin hali domin wa’adin kwana ukun da aka ba su ya yi kadan su nemi wani matsugunin kana da kudin da za su biya kudin shagunan da za su kama.
A nashi jawabin, shugaban hukumar tsare-tsaren na Jihar Malam Ismail Umar Dikko ya bayyana cewa dama sun sanar da su cewa babu gudu babu ja da baya a kan wannan bukata na su, domin sun lura cewa ‘yan kasuwar bawai suna da bukatar a gyara kasuwar bane illa so suke ta ci gaba da zama a hakan.
Ya ce ” mun samar musu da wani wuri anan kusa da kasuwar inda muke da wani fili biyu, sannan da wani wajen a unguwar Mu’azu, toh amma mun lura su ba wannan ba ne damuwarsu illa kawai aikin ne kawai ba sa so a yi, don mun dade muna ta tattaunawa a kan hakan da shugabanninsu to, amma abun ya citura, shi yasa muka dauki wannan matakin.
Dikko, ya kara da cewa lokacin da za a rushe kasuwar Kawo, an ba ‘yan kasuwar wa’adin kwana bakwai wanda daga baya aka kara musu kwana uku saboda sun amince da zasu koma wajen da aka tanadar musu kuma da suka kawo korafi na rashin isasshen waje da wurin Sallah da bahaya, sai aka kara musu wajen kana aka samar musu da bukatunsu, toh amma su yan Kasuwar barci ba hakan ne bukatunsu ba.
Kodayake idan ba a manta ba, gwamnatin jihar ta taba ba yan Kasuwar Barcin wa’adin kwana goma wanda jin hakan ne ya sanya ‘yan kasuwar suka maka Gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufa’i a kotu inda ake ta shari’a har yanzu ba a kammala ba sama da tsawon shekaru biyu, sannan ‘yan kasuwar sun kasance daya daga cikin mutanen da suka yiwa ita gwamnatin mai ci ruwan kuri’u a zaben farko kamin daga baya su juya mata baya a sakamakon zancen rushe kasuwar da ta yi don gina wata kamin zabenta na biyu.