Isah Ahmed Daga Jos
MA’AIKATAN Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, sun zabi sababbin shugabannin kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Najeriya [NULGE] reshen Karamar hukumar. Ma’aikatan sun gudanar da zaben sababbin shugabannin nasu ne, a sakatariyar Karamar hukumar da ke garin Saminaka.
Sababbin shugabannin da aka zaba, sun hada da Jamilu Sani a matsayin shugaba, da Bako Kawu mataimakin shugaba da Ahmed Abdullahi Sakatare, da Stephen Garba mataimakin Sakatare da Abdul Munka’ila Ma’ajiyi, da Aqilu Yarima Dattijon qungiya da Serah Ishaya shugabar mata.
Sauran sune Nura Abdullahi mai binciken kuxi da Hamisu Ibrahim wakilin sashin harkokin mulki da kuxi, da Usman Yet wakilin sashin ayyuka da Sama’ila Ahmed Wakilin sashin noma da Salmanu Umar wakilin sashin ilmi da walwala, da kuma Ibrahim Jamilu Abubakar shugaban matasa na ma’aikatan.
Da yake jawabi a wajen Daraktan ma’aikata na Karamar hukumar Lere, Alhaji Adamu Gubuci ya bayyana matukar farin cikinsa kan yadda aka gudanar da wannan zabe lafiya.
Ya yi kira ga sababbin shugabannin da aka zaba su yi adalci, kan wannan zabe da aka yi masu.
Ya yi addu’a ga shugabannin kan Allah ya taimakesu kan wannan aiki da aka dora masu, kuma ya sanya su gama lafiya.
A nasa jawabin Shugaban kungiya ma’aikatan kananan hukumomi ta Najeriya [NULGE] reshen Jihar Kaduna Kwamared Rayyanu Isiyaku Turunku ya bayyana cewa babu shakka ma’aikatan karamar hukumar Lere, sun zabi shugabannin da suke so. Don haka ya yi fatar shugabanni za su tallafa wa ma’aikatan wannan karamar hukuma.
Shugaban ma’aikatan, wanda shugaban kungiyar ma’aikatan Karamar Hukumar Birnin Gwari, Kwamaren Shu’aibu Jibrin ya wakilta, ya yi kira ga ma’aikatan su rika zuwa aiki kan lokaci kuma su rika zama a wurin aiki, har zuwa lokacin tashi.
Ya yi kira ga ma’aikatan kananan hukumomi na jihar Kaduna, su ci gaba da kasancewa masu biyayya kamar yadda da aka san su.
A nasa jawabin a madadin wadanda aka zaba sabon shugaban kungiyar Jamilu Sani ya mika godiyarsu ga Allah, da dukkan ma’aikatan wannan karamar hukuma, kan wannan zabe da aka yi masu.
Ya ce babu shakka wannan wata rana ce mai matukar tarihi a gare mu, saboda jama’a sun fito sun zabi shugabannin da suke bukata.
Ya ce saboda kyakyawan zaton da ake yi masu ya sa aka zabe su, don haka da yardar Allah za su ba marada kunya, wajen ganin sun gudanar da ayyukan su tsakani da Allah.
Ya yi kira ga ma’aikatan su ci gaba da ba su goyan baya da hadin kai kuma su ci gaba da yi masu addu’a.
Hakika mai katan karamar hukumar lere yanzune suka zabi shuwagaban nin ma aikata masu son cigaban karamar hukumar Allah ya tayaku riko jamilu sani Ang mela