Jami’an Kula Da Aikin Hajji Na Kananan Hukumomin Jihar Kano Sun Gamsu Da Shirye-Shiryen Hajjin 2020.

0
395
Daga Jabiru A Hassan, Kano.


Jami'an kula da Aikin Hajji na yankunan kananan hukumomin jihar Kano 44 sun bayyana gamsuwar su bisa yadda hukumar jin dadin alhazai ta jihar take aiwatar da shirye-shiryen aikin Hajjin wannan shekara ta 2020 tareda sanar da cewa hakan zai sanya a sami nasarar gudanar da Hajjin bans cikin nasara.

Wannan bayani ya fito ne daga jami'in alhazai na karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Shehu Datti a zantawar su da Gaskiya Tafi Kwabo, inda ya jaddada cewa daga yadda aka fara shirye-shiryen Hajjin bana a Kano, da yardar Ubangiji za'a yi aiki mai tsafta kuma cikin nasara duba da yadda su kansu maniyyatan suke fahimtar tsare-tsaren aikin Hajji.

Alhaji Shehu Datti ya kara da cewa maniyyata dake yankunan kananan hukumomi 44 na jihar Kano suna samun horo da ilimantarwa kan aikin Hajji musamman yadda ake basu bitoci da wayar da kai kan ka'idojin aikin da dokokin kasar da zasu da kuma makamar ita kanta tafiyar wanda hakan abin jin dadi ne.

Dangane da maganar biyan kudaden ajjiya kuwa, Alhaji Shehu Datti yace maniyyata suna kokari sosai wajen kai kudaden su inda ya bada misali da cewa a karamar hukumar sa ta Dawakin Tofa akwai maniyyata fiye da 35 da suka bada nasu kudin ajjiyar, sannan kuma suna cika dukkanin sharuddan da aka Santa masu cikin biyayya da sanin ya kamata.

Jami'in alhazai ya godewa hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano bisa jagorancin Alhaji Mohammed Abba Dambatta bisa yadda hukumar take kara damarar gudanar da Hajjin bana  tareda jinjinawa jami'ar yada labarai ta hukumar, Hajiya Hadiza Abbas Sanusi saboda kokarin da take yi wajen wayar da kan maniyyata kan tsare-tsaren a hukumar ke fitowa dasu domin a fahimci yadda abubuwa suke sosai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here