Kungiyar Kafofin Yada Labarai A Jihar Yobe Ta Taya Sabon DG Murnar Nada Shi

0
422
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
KUNGIYAR manema labarai a jihar (Yobe Correspondents’ Chapel) ta taya sabon Darakta Janar Na ‘yan Jaridu da kafofin yada labarai Na gwamna Buni Alhaji Mamman Muhammad  murnar nada shi kan wannna matsayi da gwamnan ya yi wato a matsayin mai magana da yawun sa wanda mamba  ne kuma tsohon shugaban kungiyar ne, tare da bayyana shi a matsayin wanda ya cancanta da matsayi da aka ba shi.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar bayan taro da kungiyar ta gudanar mai dauke da sa hannun shugabanta, Alhaji Mohammed Abubakar na jaridar Daily Independent.
“A madadin dukkannin mambobin mu muna  taya ka murna  dangane da nada ka sabon Babban Darakta janar na yada labarai da hulda  da gidajen jaridu na ofishin Maigirma Gwamnan jihar Yobe, Hon. Maimala Buni’ ya yi”
“Har wayau kuma, za mu yi amfani da wannan dama wajen ci gaba da aiki tare hadi da cikakken goyon bayan da ya dace na ilahirin  mambobin kungiyar.”
Da yake bayyana godiyar sa ga dimbin jama’ar da su ka taya shi murna tare da addu’o’in samun nasara, Alhaji Mamman Mohammed ya bayyana yadda dubun-dubatar yan uwa, abokanai da makusanta da waxanda aka daxe ana aiki tare- musamman a kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) bisa ga kauna da soyayyar da suka nuna masa tare da nuna cikakken goyon baya a hanyar ci gabansa.
”Ina mika matukar godiyata gare ku, bisa yadda kuka nuna min tsantsar soyayya da kauna hadi da dimbin addu’o’in ku da kyakkyawan fatan da kuka rinja kwararo su zuwa gareni- ta hanyar kira, sakon kar-ta-kwana hadi da a kafofin sada zumunta na zamani, dangane da sabon mujami tare da amincewar da Gwamna Mai Mala ya nuna min”.
”Hakazalika kuma, ina mika godiyata ta musamman ga maigidana, Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni (Chiroman Gujba) saboda yadda ya nuna min yarda da amincewarsa wajen nada ni wannan mukami na DG.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here