KHALIFA Shehu Ahmad Tijjani Inyass ya bayar da sanarwar dage taron maulidin Shehu Ibrahim Inyass wanda Kungiyar majma’u Ahbabu Shehu Ibrahim za ta shirya a garin Sakkwato, sanarwar ta fito daga bakin mai magana da yawun Faila maulana Sheikh Mahi Cisse a cikin wata sanarwa da suka fitar.
A cikin jawaban nasa Sheikh Mahi Cisse ya bayyana cewa Khalifa Shehun Tijjani Inyass ya bada izinin dage taron ne saboda kaucewa annobar cutar CoronaVirus wanda ta addabi al’ummar duniya, ya yi kira ga “Kungiyar Majma’u Ahbabul Sheikh” da ta gaggauta dakatar da dukkan shirye-shiryen maulidin.
Idan ba’a manta ba a jiya maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi a taron manema labarai ya ba da sanarwar dage taron maulidan guda biyu wanda za a yi a Abuja da Sakkwato.
Allah ya sa hakan ya fi alhairi, Allah kuma ya kawo karshen wannan annobar da ta addabi duniya.