Manoma Sun Roki Ganduje Ya Gyara Kananan Dam-dam Don Bunkasa Noman Rani. Daga Jabiru A Hassan. Manoma dake aikin noman Rani a Dam din kunnawa dake e jihar Kano sun roki gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje da ya kara gyara matsakaita da kananan Dam-dam din dake fadin jihar ta yadda za'a bunkasa samar da abinci da kuma aiyukan yi ta hanyar noman rani domin rage kwararar al'uma zuwa cikin birane neman abin yi. Sunyi wannan roko ne yayin da Gaskiya Tafi Kwabo ta ziyarci gonakin noman rani dake Dam din kunnawa cikin yankin karamar hukumae Dawakin Tofa wadda ma'aikatar gonna da raya karkara ta tarayya ta gyara domin tsugunar da makiyaya, inda kuma suka jaddada cewa idan gwamnatin kano ta gyara matsakaita da kananan Dam-dam da ake dasu tattalin arziki zai bunkasa wanda hakan abin dubawa ne. Malam Muhammadu mai albasa wanda shine jagoran manoman rani dake dam din kunnawa,yace idan gwamnatin Ganduje ta zabi kananan madatsun ruwa ta gyara su ruwa ya zauna manoma da makiyaya zasu sami gurin zama domin yin noma da kiwo cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya kamar yadda ake gani a dam din Kunnawa inda manoma da makiyaya masu tarin yawa suke zaune cikin jin dadi da mutunta juna batare da wani rikici ba. Sannan ya sanar da cewa daga gyara wannan dam zuwa yau, anyi noman rani da cinikayyar kayan lambu har na fiye da naira miliyan 10, tareda samar da aiki ga mutane fiye da 200 wanda hakan ya taimaka wajen rage kwararar mutane zuwa cikin birane neman aiyukan yi, inda daga karshe ya sanar da cewa zasu ci gaba da yin noman rani a wannan dam domin amsa kiran wannan gwamnati na wadata kasa da abinci. A nasa tsokacin, shugaban makiyaya na wannan dam na Kunnawa Ardo Alhaji Geza ya ce tun da aka gyara wannan dam suke zaune lafiya tsakanin su da manoman wannan guri, sannan ya jaddada cewa wannan zama tsakanin manoma da makiyaya zai ci gaba da dorewa domin makiyayi bazai iya zama ba sai da manomi, inda kuma dukkanin wadannan shugabanni sun yi godiya ga daraktan jihar kano na ma'aikatar gona ta tarayya, Alhaji Muhammadu Shehu Adamu bisa kokarin da yake yi wajen ganin dam din yana samun kulawa, tareda fatan za'a kara fadada shi ta yadda zai samar da aiyukan yi ga dumbin al'uma.