Ya Zuwa Yanzu Mutum 8 Ne Ke Dauke Da Corona Virus A Najeriya

0
590

Rahoton Z A Sada

MINISTAN Ma’aikatar Lafiya na Najeriya Dokta Osagie Ehanire ya tabbatar da samun karin wasu mutum 5 dake dauke da cutar coronavirus a Najeriya. A wata hira da ya yi da manema labarai a birnin Abuja, ya ce a birnin Legas aka gano mutanen su biyar.

Cikin mutanen 5, akwai wani dan Amurka da ya shigo kasar daga iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin. Sauran kuma ‘yan Najeriya ne, ciki har da wani karamin yaro da mahaifiyarsa da suka zo daga Amurka, sai kuma wasu maza su biyu da suka dawo gida kasar Najeriya daga Birtaniyya.

Yanzu dai adadin masu dauke da wannan cuta a Najeriya ya kai mutum 8 kamar yadda ministan ya bayyana.

Tun da farko dama gwamnatin Najeriya ta ba da sanarwar tsagaita zirga-zirga tsakanin Najeriya da kasashen da cutar ta yi kamari irin su Caina, Italiya, Sifen, Koriya ta Kudu, Amurka da kuma Birtaniya har zuwa nan da makwanni 4.

Dama kafin daukar wannan matakin Majalisar Dattawan kasar ta yi kira ga
gwamnati da ta tsaigaita zirga-zirga. Hakazalika ita ma kungiyar likitoci ta kasa ta yi irin wannan kiran da ke neman a hana jiragen kasashen waje sauka Najeriya domin rigakafin cutar ta coronavirus.

Tuni dai gwamnatin Najeriya ta fidda sanarwar rufe sansanonin horar da ‘yan yi wa kasa hidima da kuma dakatar da wasannin kasa na shekara-shekara, duk a matsayin rigakafin bazuwar cutar coronavirus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here