Ma’aikatan Kiwon Lafiya Sun Zabi Sababbin Shugabanni

0
661

Isah Ahmed Daga Jos

KUNGIYAR ma’aikatan kiwon lafiya na Karamar Hukumar Lere da ke Kaduna, sun gudanar da zaben  sababbin shugabannin kungiyar, a ranar Alhamis din nan, a sakatariyar karamar hukumar da ke garin Saminaka.

Sababbin shugabannin kungiyar da aka zaba, sun hada da Abubakar I. Muhammed a matsayin shugaba da Joshua Ishaku mataimakin shugaba da Abubakar Mohammad sakatare da Inuwa Kuroki ma’ajiyi da Maiwada Alhaji Lere mai binciken kudi da Ahmed Ibrahim Muhammad  jami’in hulda da jama’a  da kuma Kande Maitala shugabar mata.

Da yake jawabi bayan da aka rantsar da sababbin shugabannin, daraktan sashin lafiya na karamar hukumar Alhaji Abdullahi Sani, ya bayyana matukar farin cikinsa, kan yadda aka gudanar da wannan zabe lafiya.

Ya yaba wa ma’aikatan kan yadda suka gudanar da wannan zabe lafiya batare da samun wata damuwa ba, sabanin jita jitar da aka rika yadawa, cewa za a sami rikici yayin gudanar da zaben.

Ya yi kira ga sababbin shugabannin su rike wannan amana da aka damka masu, tsakani da Allah wajen jagorancin ma’aikatan.

Da yake jawabi sabon shugaban kungiyar Abubakar I. Muhammed ya mika godiyarsa ga  dukkan ma’aikatan kiwon lafiyar, kan yadda suka fito suka zabe su, cikin kwanciyar hankali ba tare da samun wata damuwa ba.

Ya ce babu shakka ganin yadda aka gudanar wannan zabe, ya nuna cewa ana zaune lafiya a karamar hukuma.

Ya yi alkawarin cewa da yardar Allah za su tsaya wajen ganin, sun kwatowa ma’aikatan hakkokinsu. Don haka ya kira ga ma’aikatan, su ci gaba da ba su goyan baya da hadin kai, don ganin sun cimma wannan kuduri, da suka sanya a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here