Malamai Za Su Iya Karantar Da Almajirai Ba Tare Da Sun Yi Bara Ba-Sheikh Abubakar Bafulatani  

  0
  916

  Isah  Ahmed Daga Jos

  SHEIKH Abubakar Bafulatani shi ne ya kafa makarantar Allon nan ta Sa’adatul Abadiya  garin Jos, shekaru 46 da suka gabata.

  A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana cewa tun da ya bude wannan makaranta, almajiransa basu taba yin bara ba. Kuma ya bayyana cewa malamai, za su iya karantar da almajiransu, ba tare da suna yin bara ba. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK: Mene ne tarihin kafuwar wannan  makaranta ta Allo  ta Sa’adatul Abadiya da ka bude a wannan gari na Jos?

  Sheikh Bafulatani: To, ita dai wannan makaranta na fara bude ta ne shekaru 46 da suka gabata. Kuma na bude wannan makaranta ne a lokacin da na zo wannan gari, ina yin almajiranci. Sai na ga tun da na iya Alkura’ani mai girma, mene ne zai sanya ba zan bude makaranta ba?.  Shi ne mutumin da nake haya a gidansa, ya ba ni daki kyauta na bude wannan makaranta. Na sayo wa yarana guda biyu alluna, muka zauna a kofar gida ina karantar da su. Kafin kwanaki 10 an kawo mani yara sun kai guda 20.

  Kasancewar na yi yawo a wurare daban-daban na Najeriya,  duk inda aka sanni  sai mutane suka yi ta kawo  yaransu, daga wurare daban-daban.

  Wurare kamar Legas,Ibadan, yankin Mambila da ke Jihar Adamawa, kasar Kamaru da sauran wurare duk  mutane sun yi ta kawo yaransu wannan makaranta.

  A  takaice kafin ayi rikicin Jos, na lokacin  tsohon gwamnan Jihar Filato Joshua Dariye, almajiraina sun kai mutum 500. Amma sakamakon wannan rikici, makarantar ta watse.

  Amma yanzu da zaman lafiya ya dawo, an sake kawo mana al’amajirai daga wurare daban daban, kamar daga jihohin Nasarawa da Kaduna waxanda sun kai mutum 90, kuma dukkansu Fulanin daji ne zalla.

  Haka kuma  akwai Hausawa almajirai  da aka kawo mani  daga yankin jihar Kaduna. A yanzu dai muna da almajirai, sama da 300 a wannan makaranta.

  GTK: Yaya za ka kwatanta yanayin yadda kake karantar da almajiranka ada, da kuma yanzu?

  Sheikh Bafulatani: Gaskiya yanzu mun canza yanayin yadda muke karantar da almajiranmu. Domin ada muna karantarwa ne batare da hadda ba. Amma  yanzu mun surka da hadisan manzon Allah da sauran littafan koyar da addinin musulunci. Wato bayan yaro ya yi karatun Alkura’ani kuma ya karanci littafan addinin musulunci, domin ya san yadda zai yi ibada. Kuma mun dauko malaman makaranta na boko, mun sanya su a cikin wannan makaranta. A yanzu mun sayi wani babban gida da zamu mayar da shi makaranta, mu sanya wadannan almajirai da muke karantarwa.

  Kuma yanzu mun dauko mahaddatan Alkura’ani mutum 12  daga Maiduguri, domin su taimaka mana wajen karantar da wadannan almajirai.  Kuma mun dauki masu karantar da ilmin kwanfuta da zasu rika karantarwa a wannan makaranta.

  GTK: Yaya maganar bara ga almajiran wannan makaranta?

  Sheikh Abubakar Bafulatani: Ni tun da na bude wannan makaranta ban taba kasa ciyar da su ba, da zai sanya har su tafi bara a waje. Don haka almajiraina basu taba yin bara ba, tun da na bude wannan makaranta. Tun a baya, bare yanzu da zamani ya canza.

  Kuma ni na sani kowanne malami zai iya zama da almajiransa batare da sun yi bara ba. Yanzu ace almajirai suna bara  abin kunya ne ga malaminsu da iyayen yaran.

  A ka’idar addinin musulunci barin almajiranmu suna bara yahudanci ne. Domin ubangiji shi ne yake ciyarwa. Idan mutum ya tsaya a haka, zai gani. Tun da na bude wannan makaranta ban taba kukan abinci ba.

  GTK: To waxanne hanyoyi ne kake bi wajen ciyar da wadannan almajirai?

  Sheikh Bafulatani:  Wadansu iyayen yaran  sukan kawo  buhunan masara, amma wadanda suke zo daga nesa basa kawo komai, amma haka Allah yake rufa mana asiri, muna ciyar da su sau uku a kowace rana, wato muna basu abinci da safe da rana da daddare. Kuma idan suka yi rashin lafiya mune muke daukar nauyin jinyarsu, ba sai an aikawa iyayensu ba. Kuma kowanne yaro yana da wajen kwanciya.

  Za a iya karantar da almajirai batare da sun yi bara ba. Domin kamar ni nayi shekaru 46 ina karantar da almajiraina, ba tare da suna yin bara ba. Don haka duk sauran malamai masu karantar da almajirai a tsagayoyi, za su iya karatar da almajiransu, ba tare da sun yi bara ba. Barin almajirai suna bara karayar zuci ne kawai. Domin kowanne malami zai iya tsayawa ya jajirce ya sanya amajiransa a gaba, kuma Allah zai taimake shi. Amma bai kamata  ace karatun Alkura’ani sai an yi bara ba.

  GTK: Maye ra’ayinka dangane da matakin da wasu jihohin kasar nan suka dauka, na hana bara?

  Sheikh Abubakar Bafulatani: A ra’ayina gwamnatocin jihohin da suka dauki matakin hana bara, sun dai dai. Kowanne malami ya dauki iyakar almajiran da zai iya ciyarwa, ba tare da barin almajiransa suna zuwa bara ba. Idan malami ba zai iya ciyar da almajiransa ba, ya bar malaman da zasu iya  su yi.

  Kuma kai uba da ka haifi yara ka dibi kamar guda 10 ka baiwa malami ya tafi wani gari da su. Kuma malami kai da matarka yaran, sai sun je sun yo bara, abin da suka ci suka rage maka ka ci da matarka. Wannan akwai wulakanta kai a ciki. Manzon Allah ya ce bai kamata mutum ya wulakanta kansa ba.

  Don haka idan aka hana barar nan, za a tafi dai dai kowanne malami idan bai zai iya ba, ya bari.

  Yanzu ni da na ajiye almajiran nan da ba sa yin bara, bani nake ciyar da su ba, Allah ne yake ciyar da su.

  GKT: Wanne kira ne kake da shi zuwa ga gwamnati  dangane da almajiranci da hana bara?

  Sheikh Abubakar Bafulatani: Kira na ga gwamnatin jihohin da suka hana bara,  shi ne su taimaki almajirai. Kuma ina ga gwamnatoci su kafa doka kan dole ne yara su yi karatu. A hukunta duk uban da ya haifi yara, ya ki ya kai su makaranta.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here