An Rufe Tashar Jirgin Kasan Abuja-Kaduna

0
456

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

HUKUMAR jiragen kasan Najeriya ta dakatar da jigilar fasinjoji a jiragen kasanta na Abuja zuwa Kaduna, Legas zuwa Ibadan da sauran sassan tarayya.

Mataimakin kakakin hukumar, Yakubu Mahmoud, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Asabar, 21 ga Maris, 2020.

Ya ce “ Hukumar jiragen kasan Najeriya ta yanke shawarar dakatar da jigilar fasinjoji fari daga ranar Litinin 23 ga Maris, 2020.“

“An yanke shawarar ne sakamakon yaduwar cutar Coronavirus. Za a sanar da fasinjoji duk lokacin da aka canza shawara.“

A bangare guda, Ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya bayyana cewa an samu karin mutane 10 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.

Ministan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita ranar Asabar, 21 ga watan Maris, 2020.
Yayin da bakwai aka samu a Legas , sauran ukun na birnin tarayya Abuja.

Yanzu dai akwai jimillar masu cutar 22 a Najeriya kuma an sallami biyu da suka samu sauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here