Ana Binciken Mutane 3 Da Suka Dawo Daga Kasar Waje A Kaduna

0
417

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNATIN jihar Kaduna ta bayyana cewa tana nan tana sa idanu a kan wasu mutane uku da suka dawo Nijeriya daga kasar waje.

Ma’aikatar lafiya reshen Jihar Kaduna ta bayyana hakan a cikin wata takardar da aka aikewa manema labarai a kaduna, inda aka bayyana cewa mutane biyu sun dawo ne daga kasar Ingila, sai kuma wani daya daya dawo daga kasar Egypt da a halin yanzu suke zaune su kadai.

Kamar yadda kwamishinar lafiya Dakta Amina Mohammed Baloni ta ce mutanen ya zuwa yanzu ba su nuna alamun cutar ba amma duk da haka ana shawarartar jama’a da su kwantar da hankalin su.

kwamishinar lafiya, Dakta Amina Baloni ta bayar da tabbacin cewa cibiyar da aka tsara da kayan aiki a shirye take domin shirin kota kwana game da cutar Korona.

Takardar ta ci gaba da cewa Dakta Amina Mohammed Baloni sun tattauna da shugaban asibitin Gwamnatin koyarwa na Jiha na Barau Dikko sun kuma tattauna da asibitin koyarwa na Gwamnatin tarayya na jami’ar Ahmadu Bello da babban asibitin kunne da kuma wakilan asibitin idanu na kasa da ke kaduna domin tabbatar da aniyar kare lafiyar jama’a da aka Sanya a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here