Cutar Korona Ta Kashe Mutum Na Farko Dan Nijeriya

0
461
Mustapha Imrana Abdullahi Da Z A Sada
BAYANAN da muke samu na tabbatar da cewa an samu mutum na farko da ya mutu saboda cutar covid 19 da ake kira Korona
Cibiyar kula da yaduwar cututtuka ta Nijeriya ce ta bayyana hakan a ranar Litinin a ssahihin shafinta na tuwita domin sanar da jama’a abin da ya faru game da lamarin.
Kamar yadda hukumar kula da yaduwar cututtukan ta NCDC, ta bayyana cewa wanda ya mutun dan shekaru 67 ne kuma Namiji da ya dawo daga neman lafiya daga kasar Ingila.
Amma bayan dawowarsa sai yanayinsa na lafiya ya zama cikin wani mawuyacin hali
Wannan yanayi ne yasa iyalinsa wato wanda ya kamu da cutar suka fitar da wata sanarwar manema labarai da suka bayyana mara lafiyar da sunan Suleiman Achimugu, wanda tsohon Manajan Darakta ne na PPMC.
Sanarwar dai na dauke ne da sa hannun Abubakar Achimugu ta ce wanda ya kamu din na can wani wuri a kebe tun lokacin da ya dawo daga kasar Ingila kuma an shaida wa hukumar NCDC game da alamun cutar Covid 19 da ake gani a tare da Suleiman Achimugu.
 ” Muna bakin cikin shaida maku rasuwar ubanmu abin kaunarmu, dan uwa Injiniya Suleiman Achimugu tsohon Manajan Darakta a kamfanin PPMC
“Ya rasu sakamakon cutar Covid 19 a ranar 22 ga watan uku, 2020 ‘yan kwanaki bayan ya dawo daga kasar Ingila.
“An gwada shi an kuma same shi da cutar tuni aka dauke shi zuwa asibitin kwararru, amma ya rasu lokacin da ake duba lafiyarsa a can”. Muna neman addu’ar Allah ya gafarta masa kuma ya warkar da daukacin marasa lafiyar da suke da cutar”.
Tuni dai aka yi Jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya shimfida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here