Dana Ya Kamu Da Cutar Coronavirus — Atiku Abubakar

0
411

TSOHON mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya ce dansa ya kamu da coronavirus.

Atiku Abubakar, ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twiiter.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya cea tuni aka kai dan nasa asibitin koyarwa da ke Gwagwalada a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya inda ake masa magani.

Atiku Abubakar ya bukaci al’umma da su saka dan nasa a addu’a.

Ya zuwa yanzu dai a hukumance akwai mutum 30 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya, idan aka hada da dan Atiku kuma adadin zai kai 31 kodayake hukumar takaita yaduwar cutuka ta kasar ba ta sanar da na dan Atikun ba.

Mutanen da ke dauke da annobar coronavirus a nahiyar Afirka sun zarce mutum 1,000 a karshen wannan makon kamar yadda hukumar da ke yaki da cututtuka ta nahiyar ta bayyana.

Kasar Uganda ta bayyana mutum na farko da ya kamu da cutar a kasar inda kasar ta ce wani fasinja ne da ya zo daga Dubai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here