Daga Usman Nasidi.
GWAMNATIN jihar Legas ta ba wa dukkan ma’aikatanta daga kan mataki na daya zuwa na 12, umurnin su zauna a gida na tsawon kwanaki 14 masu zuwa.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu, ne ya sanar da hakan yayin da yake gabatar da karin jawabi a kan bullar annobar kwayar cutar corona a jiharsa ranar Lahadi.
Ya bayyana cewa ma’aikatan zasu cigaba da zama a gida ne na tsawon kwanaki 14 masu zuwa.
A cikin makon da muka yi bankwana da shine gwamnatin jihar Legas ta bayar da umarni rufe dukkan makarantu da wuraren ibada da ke jihar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da adadin masu kamuwa da kwayar cutar corona ke karuwa a jihar.