Usman Nasidi, Daga Kaduna.
DAYA daga cikin matan mai girma Gwamnan jihar Kaduna, A’isha Ummi Garba El-Rufai, ta yi karin haske game da halin da suke ciki duk da matsayin da Maigidansu yake rike da shi.
Hajiya A’isha Ummi Garba El-Rufai a hirar da ta yi da manema labarai kwanakin baya, ta fayyace abin da jama’a ba su sani ba game da iyalin Gwamnan na jihar Kaduna.
Ummi Garba El-Rufai ta nuna cewa kuskuren da jama’a suke yi shi ne yi wa Maidakin Gwamna kallon mai kudi, ta ce kowa yana tunanin matar Gwamna a Najeriya tana da tarin dukiya.
Maidakin Gwamnan ta ce: “ Mun fi jin dadin rayuwarmu kafin mijina ya zama shugaba. Ta fuskar arziki, sosai, saboda yana maida rabin albashinsa na wata cikin dukiyar gwamnati.”
“Dole kuma mu taka wa kanmu burki wajen harkar dukiya daga facaka domin gudun jama’a su rika yi mana kallon muna daukar kudi daga asusun gwamnati.” Inji Ummi El-Rufai.
Matar Gwamnan na jam’iyyar APC ta ce ba zai dace mutane su rika tunanin iyalin El-Rufai suna barna da dukiya fiye da yadda suka saba kafin zaman Maigidan nasu Gwamna a 2015.
Wani abu da ke ci wa Hajiya Ummi Garba El-Rufai tuwo a kwarya shi ne irin bukatun da ‘Yan uwa ko Abokai suke kawowa gaban iyalan Gwamna ganin cewa suke rike da tulin kudin jihar .
“Ina ganin wannan shi ne babban kuskuren da ake yi a kan matan shugabanni. Haka ‘Yan uwa sai su dauka kuna da makudan kudi ne, su rika kawo wasu mahaukatan bukatu gabanku.”
“Idan har ka ce ba ka da wadannan kudi, sai a fara kukan cewa yaya za a yi a ce suna kan mulki, amma ba za ta taimaka ba. Jama’a suna yi maka kallon inda ba ka kai ba” Inji Ummi.
Wani abu da ba a sani ba shi ne, matar Gwamna ba za ta iya juya Jami’an gwamnati ba. “ Ina auren Gwamna, amma ba za ka zo wurina ka ce in fada wa Kwamishina ya yi maka wani abu ba.”
Ta ce ba ta da karfin ikon da za ta umurci Kwamishinan Maigidanta da ya yi wa mutum wata alfarma, ta ce har ta saba da cewa jama’a a’a ba tare da ta ji ta yi laifi ba.