Daga Usman Nasidi.
JAMA’AR Daura da ke jihar Katsina a ranar Asabar sun fada addu’o’i don neman kariya daga sabuwar mugunyar cutar coronavirus.
Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouq, ya jagoranci mazauna garin sallah ta musamman don rokon Ubangiji kariya daga cutar.
Sarkin mai shekaru 84 ya ja sallar ne a farfajiyar fadarsa. Ya bukaci mazauna garin da su kalli muguwar cutar da wata jarabawa daga Allah.
Ya yi kira ga jama’a da su tsananta addu’ar neman kariya daga cutar da sauran cutukan da ke kashe jama’a.
Sarkin ya kwatanta wannan cutar da hatsarin da ya fi na Boko Haram, ya kuma yi addu’ar cewa Ubangiji ya kawo karshen wannan masifa da gaggawa.
Ya yi umurni ga dukkan malaman makaratun allo da na Islamiyyu na kowacce mazhaba a kan su rufe makarantunsu tare da biyayya ga dukkan umurnin gwamnati.