Shugaban Hukumar Tabbatar Da Gaskiya Kan Kwangiloli Ta Jihar Bauchi Ya Yi Kokari

0
504
Injiniya Joshua Titus Gumau

Isah Ahmed Daga Jos

SHUGABAN kungiyar wayar da kan matasa ta Karamar Hukumar Toro, da ke jihar Bauchi Sani Muhammed, ya yaba wa shugaban hukumar tabbatar da gaskiya wajen bayar da kwangiloli ta jihar Bauchi Injiniya Joshua Titus Gumau kan kokarin da ya yi wajen gudanar da ayyukansa, a cikin kwanaki 100 da ya yi yana rike da wannan hukuma.  Sani Muhammed ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya  ce saboda ganin  kokari da hazakar wannan mutum ya sanya gwamnatin jihar Bauchi, ta dauko shi ta ba shi wannan matsayi.

Ya ce daga lokacin da aka ba shi wannan mukami zuwa yanzu, ya kawo canji a wannan hukuma, kuma an sami cigaba mai tarin yawa.

Ya ce duk da matsalolin da ya tarar a  hukumar da zuwansa ya gyara motocin aiki, na hukuma da suka lalace. Kuma ya sayo  na’urorin kwanfuta ya sanya wa ma’aikatan   hukumar, don ayyuka su tafi daidai. Kuma yana tafiya da ma’aikatansa a dukkan ayyukan da ake gudanarwa a hukumar.

Ya ce tun da ya zo wannan hukuma, ya tsaya wajen ganin ya tabbatar da  kudaden da aka ware, don gudanar da ayyukan raya kasa a jihar Bauchi,  an yi amfani da su  bisa ka’ida,  kamar yadda aka rubuta.

Ya ce Injiniya Titus Gumau mutum ne da ya dade yana gwagwarmayar siyasa da taimaka wa al’umma, ta fannoni daban-daban a karamar hukumarsa ta Toro.

‘’ Ya taimaka wa harkokin ilmi ta hanyar gina azuzuwa a makarantu daban-daban na karamar hukumar. Ya gina rijiyoyin burtsatse da dama. Kuma ya dauki nauyin biya wa yara kudaden makarantu tare da  daukar nauyin shirya gasar wasanni daban-daban da koya wa matasa sana’o’i daban-daban a  karamar hukumar’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here