Daga Usman Nasidi.
HUKUMAR birnin tarayya, Abuja , ta ce za a killace dukkan mutanen da aka gano cewar sun taba gawar marigayi Abba Kyari, tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.
Mukaddashin sakatare a ma’aikatar lafiya ta Abuja, Mohammed Kawu, ya ce sun gano mutanen da su ka yi aikin binne gawar marigayi Kyari.
Ya bayyana cewa za a killacesu tare da gudanar da gwajin kwayar cutar covid-19 a kansu.
Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke cigaba da nuna fushinsu a kan yadda manyan hadiman gwamnati da sauran jama’a su ka yi watsi da dokokin dakile yaduwar cutar covid-19 yayin jana’izar Kyari.
Tun kafin fitowar wannan sanarwa, rahotanni sun bayyana cewa an hana wasu manyan hadiman shugaban kasa, Muhammadu Buhari, shiga Villa bayan sun dawo daga jana’izar marigayi Abba Kyari.
Jana’izar Abba Kyari
Dumbin mutane ne su ka halarci makabartar da aka binne Abba Kyari, yawancin mutanen basu saka takunkumin rufe fuska ko safar hannu ba a matsayin matakin kare yaduwar annobar cutar covid-19.
Akwai fargabar cewa jama’ar sun yi watsi da shawarar NCDC, lamarin da zai iya haifar da yaduwar kwayar cutar covid-19 saboda da yawan jama’a da su ka halarci binne marigayi Abba Kyari.
Tun bayan bullar annobar cutar covid-19 a Najeriya aka saka dokokin hana taron jama’a da yawansu ya haura 20 tare da umartar jama’a su zauna a gidajensu don dakile yaduwar cutar.