NULGE Ta Tallafa Wa Ma’aikatan Yankin Lere Da Bashin Kayayyakin Abinci Don Yin Azumi

0
601
Kwamared Jamilu Sani Shugaban Kungiyar Ma'aikatn Karamar Hukumar Lere

Isah Ahmed Daga Jos

GANIN irin matsanancin halin rayuwar da ake ciki, sakamakon dokar hana fita da aka sanya a Jihar Kaduna,  da kuma zuwan Azumin watan Ramadan. Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Najeriya [NULGE], reshen karamar hukumar Lere da ke Jihar Kaduna,  ta yi kokarin samar wa ma’aikatan karamar hukumar, bashin kayayyakin abinci da suka hada da shinkafa buhuna 450 da taliya katan 800 da manja jarka 200, da kuma  man gyada jarka 200. Kan farashi mai rahusa, don su sami saukin gudanar da Azumin wata Radaman.

Da yake zantawa da wakilinmu a wajen da suke rabawa ma’aikatan wadannan kayayyakin abinci, a garin Saminaka. Shugaban kungiyar Kwamared Jamilu Sani Sani, ya bayyana cewa  ganin matsanancin halin rayuwa da ma’aikatan suka shiga sakamakon dukar hana fita, sannan kuma ga Azumi ya zo, saku hada hanu da wasu ‘yan kasuwa, suka samowa ma’aikatan wadannan kayayyaki.

Ya ce duk da ana biyan albashi, idan ma’aikaci baya fita ba zai sami rauni, saboda zaman gida. Sannan kuma ga Azumi ya zo ga  kuma ma’aikaci ba shi da abincin da zai ciyar da iyalasa, don haka za a iya samun matsala.

Ya ce wadannan kayayyakin abinci sun hada da shinkafa buhu 450  da taliya katan 800 da manja jarka 200  da man gyada jarka 200.

‘’A shirye muke mu  cigaba da taimaka wa ma’aikatan. Don haka akwai abubuwa da dama da muka sanya a gaba, musamman  wajen ganin ma’aikatan sun daina dogara da albashi. Ta hanyar samar masu da wasu hanyoyi da za su rika yin wasu abubuwa, da za su rika  kawo masu kudaden shiga, ba wai albashi kadai ba’’

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here