Yadda Kungiyar AFAN Reshen Jihar Jigawa Ke Kawo Sauyi A Harkar Noma

0
340

JABIRU A HASSAN, Daga Dutse.

BABU shakka, kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Jigawa, bisa jagorancin Alhaji Idris Yau Mai Unguwa tana kokari wajen kawo sauyi mai amfani kan sha’anin aikin gona a fadin jihar wanda hakan ta sanya manoma suke cikin yanayi mai albarka a fannin noma don riba.

A duk lokacin da na shiga cikin jihar Jigawa, nakan fahimci yadda manoma suke kokarin gudanar da aiyukan su na noma  rani da damina tareda Samar da abinci mai yalwa bisa la’akari da bukatun gwamnatocin kasarnan na neman wadata kasa da abinci tareda samar da aiyukan yi ga al’uma musamman matasa.

Haka kuma dukkanin manoman da suke magana da yan jaridu da sauran masu aika rahotanni kan aikin noma sun nunar da cewa kungiyar AFAN tana taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba mai kyau a fannin aikin gona a jihar ta Jigawa duba da yadda shugaban kungiyar na jihar Alhaji Idris Yau Mai Unguwa yake kokari wajen lalubo dukkanin wasu hanyoyi da manoma zasu amfana da shirye-shiryen gwamnati na bunkasa noma a kasa baki daya.

Bugu da kari, shugaba Idris Yau Mai Unguwa yayi fice wajen kyautata dangantaka mai kyau tsakanin manoman jihar Jigawa da gwamnatin jihar da gwamnatin tarayya  da su kansu hukumomin bincike da wayar a kan manoma kan yadda zasu ci gaba da gudanar da aiyukan noma mai albarka.

Wadannan nasarori suka sanya uwar kungiyar ta AFAN bisa jagorancin Alhaji Kabir Ibrahim take kallon jihar Jigawa a matsayin daya daga cikin jihohi wadanda suke da dukkanin abubuwan da suka wajaba na samun duk wani tallafi walau daga gwamnatin jihar Jigawa ko gwamnatin tarayya ko kuma wasu cibiyoyi na bunkasa noma a jihar.

Wadannan nasarori ya sanya kafafen yada labarai suka himmatu wajen bayyana yadda ake comma nasarar bunkasa noma kuma za’a ci gaba da bayyana irin nasarorin da kungiyar AFAN reshen jihar ta Jigawa ke samu bisa shugabanci na adalci wanda shugaban kungiyar Alhaji Idris Yau Mai Unguwa keyi wanda kuma yake gamsar da daukacin manoman jihar wadanda suke bayyana godiyar su.

A karshe, kungiyoyin manoma dake fadin jihar ta Jigawa suna amfani da wannan dama wajen jinjinawa Alhaji Idris Yau Mai Unguwa tareda mataimakan da saboda kokarin da suke yi wajen hada kan manoma da kuma yi masu jagoranci mai kyau kamar yadda ake gani a fadin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here