Daga; Usman Dan Gwari.
BABU shakka, tun lokacin da muka karbi ragamar tafiyar da harkokin kungiyar yan gwari a Jihohin Kano da Jigawa ake samun nasarori wajen hada kan masu sana’ar noma da saye ko sayar da kayan gwari tare da samar da aiyukan yi wanda ta sanadiyyar hakan tattalin arzikin kasa ke kara bunkasa.
Haka kuma muna gamsuwa sosai da yadda harkokin cinikayya da kasuwancin kayan gwari ke tafiya tsakanin kudancin wannan kasa da kuma Arewa ke ci duba da yadda kowane bangare suke hada-hadar su ba tare da wata matsala ba.
Bugu da kari, a dukkanin kasuwanci da fagen da ake sauke kayan gwari dake Jihohin Kano da Jigawa, al’umma suna ta kokari wajen ganin harkokin cinikayya da safarar kayan gwari suna tafiya cikin nasara duba da yadda Allah ya sanya albarka cikin lamarin nomawa da sayar wa ko sarrafa kayan gwari.
A matsayina na shugaban kwamitin rikon kwarya na kungiyar yan Gwari ta kasa a Jihohin Kano da Jigawa, zamu ci gaba da hada hannu da sauran yan kwamitin namu wajen kara bullo da hanyoyin bunkasa nomawa da saye ko sayar da kayan Gwari a dukkanin hurumin shugabancin mu, ta yadda kwalliya zata kara biyan kudin sabulu.
Sannan kuma zamu yi kokarin kyautata dangantakar mu tsakanin mu da abokan huldar mu na kudancin kasarnan domin samar da sahihiyar hanyar gudanar da hulda tsakanin sassan, musamman ganin cewa Najeriya kasa daya ce kuma tun da dadewa ake gudanar da huldar arziki tare.
A karshe ina godiya ta musamman ga mutane da kungiyoyin yan kasuwa da manoma da kuma bangaren gwamnati saboda kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin mu, sannan ina fata Allah ya kara mana zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma karuwar arziki a kasarmu Najeriya baki daya.
Alhaji Usman B. Dan Gwari, Shugaban Riko Na Kungiyar Yan Gwari A Jihohin Kano Da Jigawa. (08034003230)