A MATSAYINA na dan Jihar Jigawa mai albarka, wanda kuma yake kaunar Jihar da al’ummar ta, Ina mai yin sako na musamman ga al’ummar Jihar masu albarka da mu hadu mu zabi Malam Umar Namadi Dan Modi a matsayin Gwamnan Jihar mu a zaben shekara ta 2023.
Kowa ya yarda cewa sashe na 39 na kundin tsarin mulkin kasarnan ya baiwa kowa damar fadar albarkacin bakin sa a tsarin dimokuradiyya, ina mai amfani da wannan kafar labarai mai tsohon tarihi ta “Gaskiya Tafi Kwabo”, domin yin Kira ga daukacin al’ummar Jihar Jigawa da mu hadu mu zabi Malam Umar Namadi Dan Modi a matsayin wanda zai gaji Gwamna Badaru Abubakar domin rabauta da ribar dimokuradiyya.
Babu shakka, munga yadda Gwamnatin Muhammadu Badaru Abubakar ta jagoranci Jihar Jigawa Kuma munga irin abubuwa na alheri da su ka wanzu wanda ko shakka babu munga alheri kuma a fannoni daban-daban na zamantakewar al’umma, sannan an samu ci gaban tattalin arziki da bunkasar noma da zaman lafiya.
Haka kuma munga yadda aka yi zama na mutunta juna da girmamawa tsakanin mai girma Gwamna Badaru Abubakar da mai girma mataimakin sa, kuma dan takarar mu na Gwamna, Malam Umar Namadi wanda sakamakon wannan zaman lafiya da suka yi, aka sami ci gaba mai kyau a Jihar mu ta Jigawa.
Na hakikance cewa idan muka zabi Malam Umar Namadi Dan Modi a matsayin wanda zai gaji Gwamna Badaru Abubakar a zaben 2023, da yardar Allah za mu sami karin ci gaba a Jihar musamman ta fannin noma da wadata kasa da abinci. Ina Kira ga wadanda su ka yi katin zabe basu karba ba da su yi kokarin mallakar katin su na zabe domin ganin an zabi shugabanni nagari a Jihar Jigawa.
ALHAJI IDRIS YAU MAI UNGUWA (Jaga), Shugaban Kungiyar AFAN, Jihar Jigawa.