JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
KUNGIYAR kare martabar Dimokuradiyya da tabbatar da shuganaci nagari, wato “Movement For The Democratic Support And Good Governance” (MSDG), ta jinjinawa shugaban kasa muhammadu Buhari saboda kafa kwamitin mika mulki da ya yi.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis a Jihar Kano, wanda shugaban ta na kasa, Alhaji Dauda Mohammed Ali ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai, ta yi marhabin da matakin da shugaba Buhari ya dauka wajen kafa kwamitin kuma a lokacin da ya dace.
“Mun gamsu tare da yin marhabin da wannan tsari na kafa kwamitin mika mulki daga zababbiyar gwamnati zuwa wata zababbiyar gwamnati domin fara tsare-tsaren mika mulki cikin nasara, wanda hakan ya tabbatar mana da cewa gwamnati ta Muhammadu Buhari tana kokari wajen kara dora dimokuradiyyar wannan kasa kan ingantaccen dandamali” Inji MSDG.
Haka kuma kungiyar ta yi gargadi ga dukkanin wadanda suke son lalata tsarin dimokuradiyyar kasar, da masu yunkurin kawo rudani game sha’anin zabe ko ita kanta siyasar kasar da su ke cewa jefa kasar cikin rashin tabbas a harkar zaben da ake shirin gudanarwa, tare da fatan cewa za a yi zabuka cikin kwanciyar hankali.