Dokta Sabo: Jagora Mai Kokarin Sauke Nauyin Al’ummar Sa

0
149

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

BABU shakka shugabanci abu ne mai matukar wahalar gaske da idan aka duba irin kalubalen da ke cikin sa musamman a wannan zamani da muke ciki na mulkin dimokuradiyya.

Sai dai duk da haka, ana samun wasu shugabanni wadanda Ubangiji Ya baiwa jimirin kwaramniyar mulki tare da kokarin aiwatar da aiyukan alheri ga al’ummar su duk da irin matsalolin da shugabanni wannan karni ke fuskanta.

Cikin shugabanni da Allah Ya baiwa juriya da jimirin shugabanci, akwai zababben shugaban karamar hukumar Bichi, Dokta Yusuf Mohammed Sabo, wanda tun da Allah Ya bashi shugabancin wannan karamar hukuma yake bakin kokarin sa wajen aiwatar da aikace-aikace a fadin yankin a fannoni na zamantakewa.

Dokta Sabo ya kasance jagora mai zummar gudanar da abubuwan da al’ummar karamar hukumar sa za su amfana bisa yin la’akari da bukatun kowane bangare, wanda hakan ake bukata ga kowane shugaba wanda ake yi masa kyakykyawan zaton yin jagoranci ingantacce.

Lokaci ba zai bari a fayyace dukkanin nasarorin da Dokta Yusuf Mohammed Sabo ya samu ba, amma ko shakka babu ya yi rawar gani a fannin aiyukan Raya kasa da bunkasa fannin kula da lafiya da harkar ilimi da tattalin arziki da kuma samar da hanyoyi na dogaro dakai.

A wannan batu, wajibi ne a jinjinawa Dokta Yusuf Mohammed Sabo saboda kokarin da yake yi wajen bunkasa yankin sa duk da cewa karamar hukumar Bichi ya kunshi manyan yan siyasa da yan kasuwa da masu ilimi da kuma jam’iyyu mabambanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here