Kasuwar Zamani Ta Bichi Ta Sami Sabon Suna Daga Karamar Hukumar

0
103

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

MAJALISAR  Karamar hukumar Bichi ta sanyawa kasuwar da aka mayar ta zamani sunan marigayi Alhaji Kabiru Abubakar Bichi, tsohon dan majalisa kuma tsohon kwamishina sannan mahaifi ga dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi, Injiniya Abubakar Kabir Abubakar.

A cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman kan sadarwa da yada labarai na shugaban karamar hukumar ta Bichi, Malam Abubakar Muktar Ibrahim ta fitar, ta bayyana cewa majalisar karamar hukumar ta Bichi bisa jagorancin Dokta Yusuf Mohammed Sabo ta yanke shawarar sanya sunan marigayi Alhaji Kabiru Abubakar ne duba da irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ciyar da yankin gaba.

Sannan ta bayyana cewa Gwamnatin Dokta Yusuf Mohammed Sabo zata ci gaba da karrama mutanen karamar hukumar Bichi domin nuna godiya ta musamman dangane da irin kokarin da suka yi wajen ganin karamar hukumar ta bunkasa kamar yadda ake gani a yau.

Haka kuma sanarwar ta kuma nunar da cewa kasuwar ta Bichi wadda ta ke da tsohon tarihi, ta sami sabuntawa ne bisa kokarin da dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar, Injiniya Abubakar Kabir Abubakar ya yi na ganin an sabunta kasuwar ta yadda zata dace da zamani.

A karshe, sanarwar ta jaddada cewa za a yi rabo na gaskiya da adalci ga masu shagunan da sabunta kasuwar ta shafa ta yadda kowane dan kasuwa zai gamsu da yadda rabon shagunan zai kasance.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here