Daga; IMRANA ABDULLAHI, Kaduna.
GWAMNAN Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya kwace takardar wasu kaddarori guda tara (9) mallakar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Ahmad Muhammad Makarfi wanda Gwamnatin Jihar ta mallaka mishi ada.
Su dai wadannan Kaddarori na tsohon Gwamna Makarfi tuni har an yi masu lambar za a rushe su gaba daya.
Sanarwar takardar soke takardar mallakar da aka ba tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Ahmad Muhammad Makarfi, tuni aka mikawa mahukuntan wadannan kaddarorin a ranar Alhamis, a garin Kaduna.
Takardar sokewar dai na dauke da sa hannun Muhammad Aminu Sakataren ma’aikatar da ke kula da harkokin Filaye a Jihar Kaduna (KADGIS), yayin da aka rubutawa Ibrahim Makarfi, Darakta a kamfanin Canes da ke kula da kaddarorin, da ke a harabar Dandalin Murtala mai dauke da lambar filoti 11 a unguwar Doka cikin garin Kaduna.
Kaddarorin da abin ya shafa sun hada da fulotai guda biyar a Magadishu, sai filotai uku a kan tatin Kwato da kuma filoti daya a Doka wanda dukkansu a cikin garin Kaduna su ke.
“An ba ni umarni ne da in rubuta takarda game da damar mallakar Filaye in kuma sanar da kai cewa Gwamnan Kaduna ya ce a cikin irin ikon da doka ta bashi karkashin sashe na 28 kuma biyar cikin baka (5) (a) da (b) na dokar amfani da fili ta shekarar 1978, ya kwace ya kuma soke damar mallakar da kake da ita”, a cewar takardar.