Hukumar NDLEA Ta Kama Mutane 85 Bisa Zargin Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi

0
40

Daga; IMRANA ABDULLAHI.

A RANAR Litinin da ta gabata, hukumar da ke yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a Jihar Kano, ta kai samame wani dandalin da wasu da ake zargi da shiga wani Kulab din Dare suna yin ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai a Kano mai dauke da sa hannun Abubakar Idris Ahmad, Kwamandan hukumar ta NDLEA a Jihar Kano, inda ya bayyana cewa dalilin kai samamen ya biyo bayan irin korafe- korafen da ake samu ne a kan Kulab din na masu yin ta’ammali da miyagun kwayoyi a wurin.

Ya ci gaba da cewa mutanen da suke kusa da wannan wurin ne wato Kulab din suka kai kokensu cewa an mayar da wajen wurin harkar miyagun kwayoyi.

Ya kara da cewa tuni har sun samu nasarar kame mutane Maza 55 da Mata 30 da kuma wadanda ake zargi da harkar sayar da tabar Wiwi da aka samu tare da su.

Idris Ahmad, ya tabbatar da cewa sun kuma samu nasarar kama wadanda suka yi niyyar tserewa ta hanyar tsallake Katanga, ko kuma boyewa a cikin Na’urar sanyi Firij, amma an yi nasarar kama su.

Ya ce, “wannan nasara ce ga hukumar NDLEA da suke yaki da sha tare da fataucin miyagun kwayoyi a Jihar Kano”.

“Ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma safarar mutane da na mummunar illa ga harkokin jama’a baki daya.

“Ana nanana yi masu tambayoyi domin a gano wadanne ne dilolin miyagun kwayoyi a cikinsu kafin a kaisu gaban kuliya.

“Masu yin amfani da miyagun kwayoyi za a mayar da su duk su koma mutanen kirki ta hanyar ba su shawarwarin da suka dace”, inji Idris Ahmad.

Idris ya kuma yi kira ga daukacin al’umma da su hanzarta kai rahoton dukkan mutanen da ake zargin suna yin ta’ammali da miyagun kwayoyi zuwa ga hukumarsu domin daukar matakin da ya dace, saboda babu wurin da dilolin miyagun kwayoyi za su boye a Jihar Kano baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here