A Fito Da Hujjar Da Ke Kalubalanta Ta, Shugaban EFCC Ya Mayarwa Matawalle Martani

0
60

Daga; IMRANA ABDULLAHI.

SHUGABAN hukumar EFCC a tarayyar Najeriya, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Zamfara ya Fito da hujjar da yake da ita a kan batun neman cin hanci da ya yi masa.

Matawalle ya yi kira ga shugaban hukumar ta EFCC da ya ajiye aikinsa, inda ya bayyana cewa shugaban hukumar EFCC akwai wadansu tambayoyin da ya dace ya amsa game da batun cin hanci.

A cikin wata takardar sanarwar da shi kansa ya sanya wa hannu a ranar Laraba, Gwamna Matawalle ya zargi Bawa na EFCC da batun Cin hanci domin kawai ya mayar da kansa mai kudi, dalilin da ya sanya yake kira ga shugaban na EFCC da ya sauka daga mukaminsa domin ya mika kansa a gudanar da bincike.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta binciki Bawa da kuma ayyukan da hukumar EFCC ke aiwatarwa a karkashinsa.

Ya ce; “Ni da wasu muhimman mutane a Najeriya muna da hujjojin cin hanci, da kuma aikata laifi a cikin ofishin aikin Gwamnati da laifin wulakanta ofis a kan shi (Bawa) da kuma hukumar EFCC a karkashinsa.

Ita dai hukumar EFCC ta ce tana gudanar da bincike ne a kan Gwamna Matawalle game da zargin dibar dukiyar jama’a, bayar da kwangiloli da kuma karkatar da kudi naira biliyan 70.

Amma dai a lokacin da yake tattaunawa da gidan rediyon BBC Hausa, Bawa ya ce hakika abu ne mai amfani da kuma taimakawa Matawalle ya fito da hujjojinsa na zarge-zargen da yake yi.

“Babu wani dan adam a bayan kasa da zai ce ya na da gaskiya dari bisa dari, na karanta a inda shi Matawalle ke cewa in fadada binciken da muke yi zuwa ga ministoci.

Muna nan muna ta binciken mu kamar yadda ya dace saboda haka idan Gwamna Matawalle na da wata masaniya a kan wani minista ko kuma Gwamna da ke cikin batun aikata cin hanci da ya kai rahoto ga hukumomin da ya dace.

“Idan har ya na da hujjar batun cin hancin da yake yi mani, ai inda ya dace ya kai batun shi ne ga hukumar Yan Sanda, ICPC da hukumar kula da Da’ar ma’aikata saboda a nan ne za a iya gudanar da bincike a kan irin wadannan batutuwan na korafe korafe irin hakan”, Inji Bawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here