Mai Unguwa Bashir Rabiu Ya Yi Alwashin Hada Kan Al’ummar Sa

0
136

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

MAI Unguwar Rinji dake yankin kasar dagacin Kwa, gundumar Hakimin Dawakin Tofa, Malam Bashir Rabiu Kwa ya bayyana cewa zai yi kokari sosai wajen hada kan al’ummar sa ta yadda za a ci gaba da samun zamantakewa mai albarka.

Ya yi wannan bayani ne a zantawar sa da wakilin mu bayan nadin da aka yi masa a matsayin sabon mai unguwar Rinji, inda kuma ya sanar da cewa kofar sa a bude ta ke wajen yin aiki da al’ummarsa ta yadda za a sami zaman lafiya da mutunta juna.

Malam Bashir Rabiu Kwa, ya kuma bayyana cewa shugabanci na Allah ne kuma Allah ke bada shi ga wanda yaso, don haka yana fata dukkanin al’ummar Rinji za su ci gaba da kasancewa a sahun gaba wajen ganin unguwar tana samun managarcin ci gaba ta kowace fuska.

Mai unguwa Bashir Rabiu, ya godewa Maimartaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero da Hakimin gundumar Dawakin Tofa, Alhaji Is’ma’il Umar Ganduje da Dagacin Kwa, Malam Muktar Magajin Kwa da kuma dukanin wadanda suke da hannu wajen ganin an gudanar da wannan nadi nasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here