Ado Tambai Kwa Ya Jinjinawa Ganduje Bisa Aiyukan Raya Kasa

0
79

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

GWAMNA Abdullahi Umar Ganduje ya sami yabo da fatan alheri daga shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwa saboda aiyukan raya kasa da ya gudanar a fadin karamar hukumar.

Da yake zantawa da wakilin mu, bayan Gwamna Ganduje ya kaddamar da wasu muhimman aiyuka a yankin ranar Juma’ar data gabata, Ado Tambai Kwa ya bayyana cewa ba za a manta da Gwamnatin Ganduje ba duba da irin aiyukan alheri da ta aiwatar a karamar hukumar bisa la’akari da bukatun al’ummar kowane bangare.

Ya ce “al’ummar karamar hukumar Dawakin Tofa sun amfana da mulkin dimokuradiyya, sannan an yi musu aikace-aikaci masu amfani don haka suna masu godiya ga Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje tare da yi masa fatan alheri.

Shugaba Ado Tambai ya kuma jaddada cewa aiyukan da Gwamna Ganduje ya yi a karamar hukumar ta Dawakin Tofa suna amfanar al’umma wadanda kuma zasu amfani ‘ya’ya da jikoki masu zuwa saboda ingancin su.

A karshe, ya yi amfani da wannan dama inda ya sanar da cewa suma a mataki na karamar hukuma, sun sami nasarori masu tarin yawa ta fuskar bunkasa ilimi da kula da lafiya da tsaro da samar da hanyoyi na dogaro dakai ga mata da matasa ba tare da nuna kasala ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here