An Koyawa Mutane 660 Sana’o’i A Funtuwa

0
58

Daga; IMRANA ABDULLAHI, Kaduna.

A KOKARIN da wasu al’umma ke yi musamman marasa galihu domin su samu damar tsayawa da kafafunsu, hakan yasa Muryar darika ta koya wa mutane dari 660 sana’o’in da za su dogara da kansu.

Bisa wannan dalilin ne ma yasa zababen gwamnan Jihar Katsana, Dr. Dikko Umar Rada ya yaba wa Muryar Darikar Tijjaniyya Funtuwa, bisa kokarinta na koyawa mutane dari shida da sitin Sana’oi dan dogara da kansu.

Dakta Dikko Umar Rada, da ya samu wakilcin Abdurahaman Nasir a wajan raton, ya bayyyana cewa wannan shi ne kudirin zababben Gwamna Rada da zarar ya shiga fadar gidan Gwamnatin Jihar Katsina.

Zabeben gwamnan, ya tabbar da cewa zai mara wa wannan shirin baya dan ganin kudirin su ya cika na samarwa alumma sana’ar yi dan dogaro da kai ba tare da jiran aikin gwamnati ba.

Shugaban sashen koya sana’o’in, Malam Nuhu Kabir, ya bayyyana cewa wannan bikin yaye daliban da Muryar Darika ta koyawa Sana’oi, ba shi ne na farko ba dan a watannin baya sun horar da mutane 210, yanzu kuma gashi sun horar da mutane dari shida da sittin da shida Sana’oi daban-daban dan dogara kai da ciyar da al’umma gaba”, injii Malam Nuhu”.

Malam Nuhu Kabir ya kuma kara da cewa, wadanda suka amfana da wannan horan Sana’oi, sun hada da Marayu, Marasa karfi, Mata da matasa kuma kowannen su shi ya zabarwa makansa sana’ar da yake da sha’awa a kan ta.

Yanzu haka sana’oi goma sha biyar ne kala daban-daban muka koyawa mutane, wadanda suka hada da Man Shafawa, Man gyaran Fata, Sabolun wanka da na Wanki, Man kitso, Man Humra da kuma maganin gargajiya da dai sauran su, inji Shugaban Malam Nuhu Kabir.

Kalifa Ali Saidu Alti da Limana Abdurahaman ne suka jagoranci taron a matsiyin su na jogogin Muryar Darika Tijjaniya da ke Karamar hukumar ta Funtua.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here