El- Rufa’I Ya Cire Sarakuna 2 Da Masu Unguwanni 2

0
69

Daga; IMRANA ABDULLAHI, Kaduna.

GWAMNAN Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya amince da cire sarakunan Arak da Piriga Jonathan Paragua Zamuna da tsohon Soja mai ritaya
Janar Aliyu Iliyah Yammah baki dayansu.

A cikin wata takardar sanarwa daga kwamishiniyar ma’aikatar da ke kula da kananan hukumomi, Umma Ahmad ta fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewa sarakunan guda biyu duk sun rasa mukaman su na sarautar gargajiya daga ranar Litinin 22 ga watan Mayu, 2023.

Kamar dai yadda Umma ta bayyana a cikin takardar sanarwar, batun cirewar ya biyo bayan irin yadda ma’aikatar kula da kananan hukumomi suka amince da shi ne kuma suka rubuto.

Kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulki da ke kunshe a cikin sashe na 11 na dokar masarautun gargajiya, doka mai lamba 21 ta shekarar 2021.

Sanarwar ta ci gaba da bayanin cewa Hakimin Garun Kurama, Babangida Sule, zai ci gaba da duba yadda abubuwa ke tafiya a masarautar Piriga, har sai an nada wani sabon Sarkin, wato (Cif).

Yayin da aka bayar da umarni ga sakataren masarautar ya ci gaba da aiwatar da aiki a kan hakan na nadin sabon Sarkin.

“Sakataren Masarautar Arak Gomna Ahmadu, zai ci gaba da kulawa da al’amuran masarautar sannan kuma ya ci gaba da gudanar da aiki kan yadda za a zabi wani sabon Sarkin.

Gwamnati ba za ta lamunta ba da irin yadda Janaral Iliya Yammah ya amsa takardar da aka bashi ta tuhuma game da yadda ya nada Hakimai hudu sabanin guda daya da aka amince masa ya nada a cikin masarautarsa da kuma rashin kasancewarsa ya na zama a masarautar Arak.

“Batun cire Jonathan Zamuna kuwa ya biyo bayan irin yadda aka samu tashin hankali ne tsakanin al’ummar Gure da Kitimi da ke a masarautar Piriga a karamar hukumar Lere da kuma rashin zamansa a masarautar “, inji takardar sanarwar.

Sanarwar ta kuma yi bayanin cewa an kuma cire mai unguwar Aban Abujan Mada da kuma Anjil a cikin masarautar Arak.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here