Ganduje Ya Rushe Majalisar Zartaswar Jihar Kano

0
33

Daga; IMRANA ANDULLAHI.

A KOKARIN da Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na ganin an mika ragamar mulkin Jihar a hannun zababbiyar Gwamnati, Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje da ake yi wa lakabi da Gandun aiki ya bayar da umarnin kowa ne kwamishina da mai ba Gwamna shawara ya ajiye mukaminsa domin tabbatar da muka mulki salim alim a Jihar.

A cikin wata takarda mai taken “Mika Madafun iko” da ta fito daga ofishin sakataren Gwamnatin Jihar Kano, mai dauke da da hannun Babbar sakatariyar Ofishin, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota ne ta bayyana hakan.

Kamar dai yadda takardar ta kunsa cewa Kwamishinoni da masu bayar da shawara tare da shugabannin ma’aikatun Gwamnati da kuma kamfanoni mallakar Gwannatin Jihar duk su mika ayyukan ofisoshin da suke rike da su ga manyan ma’aikatan da sune masu mafi girman mukamai dake ofishinsu domin su ajiye aikin.

Takarda ta bayyana cewa ayayin da wa’adin mulkin gwamna Ganduje ya zo karshe a karo na biyu, ranar 29 ga watan Mayu Shekarar 2023, kundin tsarin Mulki ya Umarce shi da ya sauke dukkan ‘Yan Siyasa masu rike da mukaman gwamnatin Jihar domin duk su ajiye aikin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here