Rikicin Filato: Fulani Sun Yi Asarar Sama Da Mutune 100 – Kungiyar Miyetti Allah

0
36

Daga; ISAH AHMED, Jos.

KUNGIYAR Fulani makiyaya ta Najeriya, (MACBAN), reshen Jihar Filato ta bayyana cewa al’ummar Fulani, sun yi asarar sama da mutum 100, a harin da aka kai a wasu kauyuka da ke Karamar Hukumar Mangu a makon da ya gabata.

Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar, mai dauke da sanya hanun Shugaban kungiyar, Malam Muhammad Nuru Abdullah.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Filato, ta tabbatar da cewa mutum 87 ne suka rasa rayukansu a wannan hari.

Itama a nata bangaren, Kungiyar al’ummar kabilar Muwaghagvul ta yi iqirarin cewa ta rasa mutum 85 a wannan hari da aka kai.

To amma, a sanarwar da Kungiyar Fulani makiyayan reshen Jihar Filato ta fitar, wadda Shugaban Kungiyar Malam Muhammad Nuru ya sanyawa hanu, ta bayyana cewa al’ummar Fulani sama da mutum 200 da suka hada da mata da kananan yara, suka bata a wannan hari. a yayinda sama da mutum 100 suka rasa rayukansu.

Har’ila yau, sanarwar ta ce dabbobin al’ummar Fulanin da suka hada da shanu, da tumaki da awaki sun bata, a yayin da aka kawo wadannan hare-hare.

“Wannan wata mummunar munafa ce, ta kisan kare dangi da aka shiryawa al’ummar Fulani, a kauyukan Bwoi da Kombun da Sarfal da Rinago da Jukga da Kuwes da Kaangag da Farin kasa da Kerana da Lugga Dimeza da Fungong da Gindiri Gok da Bughan Gida da Millet da Rufwang da Tidiu da Dejwak Rufwang da Lupo da Wushik da dai sauransu. Ya zuwa yanzu an gano shanu guda 1,000 a hanun barayin da suka sace su, tare da taimakon jami’an tsaro”.

Sanarwar ta ce a wadannan hare-haren, maharan sun yi awon gaba ko kuma kona dubban dabbobi da kayayyakin al’ummar Fulani.

“Wadannan ayyyukan ta’addanci da aka yiwa al’ummar Fulani, ya jefa su cikin mawuyacin halin da ya sanya dubbai yin gudun hijira zuwa wasu yankuna na Karamar hukumar Mangu da sauran wuraren da suke makotaka da wannan Karamar hukuma”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here