Wasu Fusatattun Matasa Sun Kashe Wanda Ake Zargi Da Satar Mashi A Garin Soba

0
57

Daga; IMRANA ABDULLAHI, Kaduna.

WADANSU Fusatattun matasa a karamar hukumar Soba da ke cikin Jihar Kaduna, sun kashe wani matashi mai shekaru 25 da aka bayyana sunansa da Sani Adamu da yake a Tashar Iche Maigana sun kuma Kona gawarsa duk bisa zarginsa da karbewa wani dan uwansa Babur kuma ya kashe shi mai suna Abubakar Haruna da ke kauyen Bauda a Maigana.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Litinin 15 ga watan Mayu, 2023, bayan da Sani Adamu ya yaudari dan uwan nasa Abubakar Haruna mai shekaru 20 inda ya kwada masa wani mabugi da nufin sace masa Babur, wanda dalilin hakan ya ce ga garin ku nan.

Wani shaidan gani da ido da lamarin ya faru a idanunsa da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru da misalin 12:30 a wannan ranar, ya bayyana cewa Sani Adamu ya cewa Abubakar ya raka shi zuwa wani kauye na kusa da su, a kan hanyar su ne ya fito da wani mabugi ya buga masa a kai, wanda dalilin hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Ya ce “a lokacin da labarin batun kwace Babur da kuma kashe Abibakar Haruna ya bayyana ga jama’a, matasan kauyen sai kawai suka yi ta tururuwa suna fito wa suka farmaki wanda ake zargin suka kashe shi tare da Kona gawarsa.

Kamar dai yadda majiyar mu ta bayyana, ta bayyana nuna cewa dukkan kokarin da jami’an tsaron Yan Sanda suka yi na ganin sun tarwatsa taron jama’ar ya ci tura, saboda tsananin yawansu da kuma irin makamai masu hadarin da suke dauke da su a lokacin.

Da majiyar mu ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar yan Sanda da ke Kaduna, DSP Muhammad Jalige cewa ya yi har wancan lokacin dai bai samu wannan rahoton ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here