Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya Ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya

0
52

Daga; IMRANA ABDULLAHI.

AN bayyana Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya a matsayin wanda ya zama Sabon zababben shugaban kungiyar Gwamnonin arewacin Najeriya.

Majiyarmu ta tabbatar mana cewa Gwamnan Gombe dai ya samu nasarar lashe zaben Gwamnan Jihar da ke jiran rantsuwa domin ci gaba da zama Gwamnan Jihar Gombe a karo na biyu, a ranar 29, ga watan Mayu.

Hakan kuma ya biyo bayan kammala wa’adin shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa ne na yanzu, Simon Bako Lalong wanda zai kammala wa’adinsa a matsayin Gwamna a ranar 29 ga watan Mayu.

Ana saran Gwamna Muhamamd Inuwa Yahaya zai shugabanci kungiyar domin ciyar ga yankin Arewacin Najeriya gaba.

Kuma wannan shugabanci da ya same shi ya biyo bayan irin yadda Gwamnan na Gombe ya samu gagarumar nasara ne a karon farko a fannonin Ilimi, lafiya da kuma tattalin arziki wanda duk sun bunkasa a Jiharsa.

Kuma kamar yadda kowa ya shaida, Jihar Gombe ce wurin da aka fi samun zaman lafiya a yankin Arewa maso gabashin Najeriya a tsawon shekarun hudu da ya jagoranci Jihar.

Zamu kawo maku karin bayani…

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here