IHR Ta Buƙaci Zababbun Gwamnoni Da Su Guji Rusa Tsarin Ayyukan Hajji Na 2023

0
89

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KUNGIYAR masu aikin hajji mai zaman kanta wato Independent Hajj Reporters (IHR), ta bukaci zababbun gwamnonin da su ci gaba da gudanar da aikin hajjin a Jihohinsu daban-daban ta hanyar kaucewa sauye-sauyen siyasa da ka iya kawo cikas ga nasarar kammala aikin hajjin bana ta 2023.

A wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Litinin, kodinetan Kungiyar na kasa, Ibrahim Muhammed, ya bayyana cewa za a fara jigilar maniyyatan Najeriya a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu, kimanin kwanaki hudu da rantsar da sabon shugaban kasa da Gwamnonin Jihohi a fadin kasar.

Kungiyar mai zaman kanta ta IHR da ke sa ido tare da bayar da rahoto kan ayyukan hajji a Najeriya da Saudiyya, ta bukaci gwamnonin da ke kan karagar mulki da su lura da halin da alhazan da suka biya kudaden ajiyarsu domin gudanar da aikin hajjin.

Sanarwar ta ce, “A yayin da muke taya sabbin zababbun gwamnonin murna da maraba da su, muna kara kira gare su da kada su canza tsarin gudanar da ayyuka na Hajjin a Jihohinsu daban-daban domin kaucewa kawo cikas ga tsarin gudanar da aiki a shekarar 2023 wanda a karshe ka iya haifar da rudani yayin tashin jirgin alhazai.

“Abin lura ne cewa an kammala shirye-shiryen gudanar da dukkan ayyukan hajji yayin da NAHCON da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihohi da Jiragen Sama na Alhazai da sauran masu gudanar da aikin Hajji suka tsara dabarun yadda za a gudanar da aikin.

Kungiyar ta lura cewa a halin yanzu akwai fargaba sosai a cikin harkokin aikin hajjin Najeriya na cewa wasu daga cikin gwamnonin da ke zuwa za su iya maye gurbin wasu daga cikin manyan jami’an hukumar alhazai a tsakiyar jigilar alhazai, wanda hakan kan iya kawo cikas ga tsarin tafiyar da alhazai.

“A duk lokacin da suka yanke shawarar aiwatar da wasu sauye-sauye a tsarin gudanarwa na hukumar alhazai, damuwarmu ita ce jin dadin alhazai, muna kira ga sabbin gwamnonin da su sanya ido a kan daukar duk wata matsaya don kada su kawo cikas ga ayyukan aikin hajji.”

“Masu kula da aikin Hajji mafi kusa da alhazai su ne jami’an hukumar alhazai ta Jiha wadanda suka yi wa maniyyatan rajista, suka gudanar da fadakarwa, suka ba su biza, suka raba musu jakunkuna da riguna.

“Wadannan ayyuka sun sa jami’an alhazai na yankin suna tuntuɓar mahajjatan kai tsaye kuma a mafi yawan lokuta suna sanin mahajjatan. Sakamakon gurbata tsarin tafiyar da alhazai na Jihar shi ne, nan take Sakatarorin zartaswa da za a nada za su zo da tawagarsu domin maye gurbin mataimakan alhazai na yankin – wadanda a baya suki kulla da alaka na mahajjatan.

Kungiyar ta ce wannan roko ya dace saboda jigilar jiragen sama na shekarar 2023 da yakin basasar Sudan ya afkuwa, tana mai cewa “a wannan lokaci, duk wata shawara da ta shafi siyasa dole ne a yi kyakkyawan tunani don kada ta kawo cikas ga aikin hajjin cikin sauki,” Inji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here