NUJ Kaduna Ta Taya Lawal Molash Murnar Zama Sabon CPS Ga Zababben Gwamnan Kaduna

0
41

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KUNGIYAR ‘yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna, ta taya Muhammad Shehu Lawal (Molash) murnar zama sabon babban Sakataren yada labarai wato Chief Press Secretary (CPS) ga sabon zababben Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa mai dauke da sa hannun shugabar Kungiyar da kuma sakatariyar kungiyar, Kwamared Asma’u Yawo Halilu da Gambo Santos, kuma aka bayyanawa manema labarai a garin Kaduna a ranar Laraba.

A jawabinta, kungiyar ta bayyana cewa Lawal yana da kwarewa da kuma iya tafiyar da kowa da kowa a cikin wannan tafiya ta sake yin tambari da sake fasalin sabuwar Jihar Kaduna karkashin Dokta Uba Sani.

A cikin sanarwar, kungiyar ta bukaci sabon magatakardar yada labarai da ya kawo hazakarsa ta basira, da’a da kuma dabi’unsa da nufin bai wa dukkanin sassan kafafen yada labarai da ke aiki a Jihar Kaduna da ma kasa baki daya.

Sanarwar ta kuma bukaci mambobin kungiyar, da masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai da su tashi tsaye tare da marawa sabon sakataren yada labarai baya wajen gudanar da aikinsa.

Kungiyar ta NUJ ta kuma yi addu’ar samun nasara da kuma kyakkyawar alaka da gwyamnatin APC mai zuwa a Jihar Kaduna don ci gaban zamantakewa da tattalin arziki da siyasa a tsakanin ‘yan kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here