Rukunin Farko Na Maniyyatan Jihar Nasarawa Sun Yi Hadari

0
44

Daga; IMRANA ABDULLAHI.

BAYANAN da muke samu na cewa rukunin farko na Maniyyatan Jihar Nasarawa da ke Arewacin tarayyar Najeriya da ke kan hanyarsu ta zuwa filin Jirgin Saman Abuja sun samu hadarin Mota.

Su dai Maniyyatan masu aniyar tafiya kasa mai tsarki, suna kan hanyarsu ne ta zuwa babban filin Jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Aziekuwe da ke Abuja, sai suka hadu da hadari a kan hanya.

Wata majiya daga hukumar Alhazai ta Jihar ta ce hadarin dai ya faru ne a ranar Laraba, a wani wurin da ake kira “kara” da ke dab da wata kasuwar Dabbobi a karamar hukumar Keffi a cikin Jihar Nasarawa lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Abuja, da nufin a ranar Alhamis 25, ga watan Mayu, 2023 su ta fi kasar Saudiyya, domin sauke farali.

Sai dai majiyar ta tabbatar mana da cewa babu wanda ya rasa ransa kuma wadanda suka samu raunuka suna wani asibiti a cikin Jihar ana duba lafiyarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here