…Ya Bukaci Su Kara Jijircewa Yayin Gudanar Da Ayyukan Su
Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.
MATAIMAKIN Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (AIG) mai lura da shiyya ta 14, Ahmad Abdulrahman, ya kai ziyarar aiki ta gani da ido ga Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kaduna a ranar Laraba 25 ga watan Mayu, 2023.
AIG Abdulrahman wanda yake lura da Jihohin Kaduna da Katsina a karkashin shiyya ta 14, ya samu kyakkyawar tarba daga kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kaduna, CP M.Y. Garba, tare da rakiyar wasu manyan jami’an ‘yan sanda a rundunar.
Da yake jawabi yayin ziyarar aikin ga Jami’an tsaro na yan Sandan Jihar, AIG ya yabawa rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna bisa nasarorin da ta samu a kwanan baya wajen dakile miyagun laifuka a Jihar.
Acewar sa, wannan ziyarar aiki ita ce karo na farko da ya kawowa Rundunar Yan Sandan Jihar bayan kasancewar AIG wanda ke kula da shiyya ta 14 domin ganawa da Jami’an yan Sandan Jihar.

Ya ce, “nazo ne domin na yi Jami’an mu gargadi tare da basu shawara a kan su kara zage damtse a kan aikinsu domin kara kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar ta hanyar aikin su.
“Ba yadda za ayi aikin yan Sanda ya yi armashi kuma ya yi natija ba tare da ladabi da biyayya ba, dole sai an rika girmama na gaba ayi musu ladabi da da’a, wanda ada idan kurata suka zauna, sun san waye na gaba a cikin su domin shi shugabanci baya tabbata sai ana biyayya.
“Sannan duk inda za a yi aiki, kai babba ka yi bibiya a kan duk wanda ka tura aiki, za ka ga idan yana yin daidai sai ka kara masa karfin gwiwa amma idan yana yi ba daidai ba, sai ka gyara masa domin komai ya daidaita.
“Abu na uku, dole ne su kawar da kai daga cin hanci da rashawa, domin idan da ba cin hanci a cikin aikin dan Sanda, toh da abin yafi haka haɓɓaka a idon mutane tare da darajar mu da girmanmu, toh don haka na jawo hankalin su a kan a daina karbe-karben Kudi har Allah Ya kawo lokacin da za a kara mana albashi domin muna da bukatar karin albashi.
Hakazalika, da yake tsokaci dangane da batun mika mulki wanda ake shirin yi a ranar 29 ga watan Mayu, mataimakin sufeto Janar na Yan Sandan, ya bayyana cewa Rundunar Yan Sanda ta kasa a shirye ta ke tsab domin ganin an kawo Kariya da tsaro cikin lumana yayin gudanar da harkokin mika mulki a kasar baki daya.
“Ni a tawa Runduna na shiyya ta 14 wacce ke kula da Katsina da Kaduna, mun shirya tsab domin kwamishinonin yan Sandan duk sun turo mun da tsare tsarensu yadda zasu gudanar da tsaro kuma ni na amince na saka musu hannu tare da kara masu karfin kwarin gwiwa na mutane da kayan aiki.
Tun da farko, a jawabinsa na maraba, CP Musa Yusuf Garba ya bayyana farin cikin Rundunar Yan Sandan Jihar bisa ziyarar aikin na gani da ido da mataimakin sufeto Janar din ya kawo musu kana da irin tallafin da suke samu daga shiyya ta 14 karkashin Jagorancin AIG Ahmad Abdulrahman.
CP M.Y Garba ya yi amfani da wannan damar wajen gargadin masu tayar da kayar baya cewa rundunar a shirye take ta tunkari duk wanda ya yi yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya da Jihar ke samu a halin yanzu.