Masari Ya Barke Da Kuka Yayin Jiwa Mambobin Majalisar Zartaswar Jawabi

0
122

…Ya ce Kwamishinoni, Masu Ba Shi Shawara, Sun yi Bakin Kokarin Su

Daga; IMRANA ABDULLAHI.

GIDAN Gwamnatin Jihar Katsina ya kasance wani wurin da ake ta koke-koke a ranar Laraba da maraice yayin da Gwannan Jihar Aminu Bello Masari ya kasa rike hawayen da ke idanunsa lokacin da yake yi wa mambobin majalisar zartaswar Jihar jawabi a wani babban taron da suka yi gabanin rantsar da sabuwar Gwamnatin Jihar a ranar 29 ga watan Mayu.

Tun da farko a cikin jawabinsa, Gwamna Masari ya bayyana cewa a cikin watan Yuni na shekarar 2015, sun sani cewa wata rana za su bar mulkin saboda haka lokacin yanzu yazo na barin Gwannatin saboda wannan shi ne taron majalisar zartaswar su na karshe tare da shi a matsayin Gwamna.

Y ce, “wannan ba shi ne karshen tashin duniya ba kuma ba shi ne karshen rayuwar mu ba. Ba mu dauki duk wani mataki ba saboda biyan bukata na kashin kan mu ba ko domin son zuciya, ko domin mu cutar da wani ko wasu ba ko domin mu kare ko hana wani ya samu wata dama ba kuma mun yi iyakar bakin kokarin mu da zamu iya yi”.

Gwamna Aminu Masari, ya godewa mambobin majalisar zartaswar bisa irin kokarinsu da jajircewarsu musamman a wajen ganin an cimma nasara.

Ya shawarci jama’a da su tabbatar da bayar da hadin kai da goyon bayansu ga Gwannati mai zuwa karkashin Dokta Dikko Radda.

Ya ce, “duk da wadansu tarnaki da wahalhalu, amma duk kowa ya dage a cikin Gwannatin nan har aka samu nasarar da aka samu cimma wa a tsawon shekaru takwas, don haka muke cewa wadannan mutane sun yi iyakar bakin kokarinsu”.

Hakazalika, shima mai bayar da shawara ga jam’iyyar APC a kan harkokin shari’a Ahmad Usman El- Marzuk, da ya kasance mai shari’a na Jihar shi ma ya barke da kuka a lokacin da yake nasa jawabinsa.

Ya ce, “Mai girma Gwamna ka wuce shugaba kawai a gare ni. Ka zamo Iba mai yi mana nunin hanya ta alkairi, dan USA la nuna Mani jin tausayi, taimako da kuma girmamawa tare da taimakawa a koda yaushe.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here