Daga; IMRANA ABDULLAHI, Kaduna.
WANI jigo shugaban al’umma a Jihar kaduna, Alhaji Ahmed Maiyaki, ya tabbatarwa da daukacin al’ummar Arewacin Najeriya da cewa kowa zai amfana da salon jagorancin da zababben Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani zai yi a Jihar.
A lokacin wata ganawar da manema labarai domin yin fatan alkairi da murna ga sabon Gwamnan na Jihar Kaduna, Alhaji Ahmed Maiyaki, ya bayyana cewa hakika ya na bayar da tabbacin cewa jagorancin da Sanata Uba Sani zai yi alkairi ne mai dimbin yawa.
Ya ce, “kasancewar Sanata Iba Sani a matsayin kwararre da ya kware a fannonin gudanar da ayyuka da kuma rayuwa daban-daban zai yi amfani da hakan domin kawo wa Jihar ci gaban da kowa zai amfana, ko a zaman Sanata Uba, a majalisar Dattawan Najeriya ya gabatar da Kudirori har guda 32 domin amfanin kasa da jama’ar baki daya, alamce da ke nuni da cewa akwai ci gaba kwarai a Jihar”.
“Tabbas hakika Uba Sani zai ɗora bisa kyawawan ayyukan da El-Rufa’i ya yi, da yin gyara a inda aka samu kuskure domin ciyar da Jihar Kaduna gaba.” Inji Maiyaki