NLC, TUC Sun Dakatar Da Yajin Aikin Da Suka Shirya Yi

0
113

Daga; IMRANA ABDULLAHI.

BAYANAN da muke samu daga tarayyar Najeriya na cewa bayan wani taron kusan sa’o’i shida tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago a fadar shugaban kasa dake Abuja, kungiyar kwadago ta kasa NLC da TUC a daren ranar Litinin din da ta gabata, sun dakatar da yajin aikin da suka shirya gudanarwa a ranar Laraba.

Ku tuna cewa kotun masana’antu ta Najeriya ta hana kungiyoyin kwadagon shiga yajin aikin da aka shirya farawa ranar Laraba.

Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ne ya sanar da kudurin taron kuma shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero ya tabbatar da hakan.

A taron na ranar Litinin, bayanan da suka gabata sun amince da cewa “Kungiyar NLC ta dakatar da sanarwar yajin aikin nan da nan don samun damar tuntubar juna.

“Kungiyoyin TUC da NLC za su ci gaba da tattaunawa da Gwamnatin Tarayya tare da tabbatar da rufe kudurorin.

“Kungiyoyin Kwadago da Gwamnatin Tarayya za su gana a ranar 19 ga watan Yuni, 2023, don cimma matsaya kan tsarin aiwatarwa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here